MUZAHARAR NEMAN A SAKI SHEIKH ZAKZAKIY A KADUNA...!!!
-KADUNA PRESS

Dubun-Dubatar 'yan uwa Musulmi ne mabiya Jagora Sheikh Zakzakiy (H) suka fito domin kara jaddada kiransu ga hukumomin Nigeria akan su gaggauta sakin Jagora (H) ba tare da wani sharadi ba kamar yadda babbar kotun da babban mai shari'a Mr. Kola wole ke jagoranta, mai mazauni a babban birnin tarayyar Nigeria Abuja ta bayar da umarni tun tsawon kusan fiye da shekaru uku da suka gabata.
'Yan uwan sunbi sahun takwarorinsu ne na sauran Da'irorin jihohin Nigeria, a yau juma'a 26/06/2020,

An fara muzaharar ne da misalin karfe uku dai-dai na rana, kuma an farota ne daga junction din kano road aka biyo titin Ahmad Bello Way aka nufin livintis round about aka gangaro ta mangal plaza aka rude muzaharar a bakin dogo junction.

Andai fara kuma ankammala lami-lafiya ba tare da wani tashin hankali ba.
-KNPRSCD 06.
-26/06/2020.