Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Taɓarɓarewar Tsaro: Buratai Ya Tare Katsina


Duk da Shugaban Sojojin kasan Nijeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai, na jihar Katsina domin dakile hare-haren yan bindiga da suka addabi jihar Katsina. A daren jiya ne yan bindigar dauke da manyan makamai suka kai hari a kauyen Bakkai, da ke gundumar Zango ta karamar hukumar Kankara, inda suka kashe mutum tara har lahira kuma ana cigaba da neman mutune da dama, wanda har zuwa daren jiya ba’a gansu ba, Kamar yadda majiyarmu ta bayyana.

Wani mazaunin garin, wanda baya so a ambaci sunansa ya shaida maba ta waya cewa ‘yan bindigar sun zo garin Bakkai da misalin karfe daya na daren jiya lahadi, inda Suka cigaba da harbe-harben kan mai uwa-da-wabi a garin, inda suka kashe mutum takwas nan take, yanzu haka muna cigaba da neman mutane da dama, da ba’a ji duriyarsu ba. Kuma sun kwashe dabbobin garin tun daga shanu da tumaki da kuma awakai sun arce da su.

Haka kuma ‘yan bindigar sun kai makamanci wadannan hare-haren a kauyukan Unguwar Madugu da kuma Kauyen Albasun Durumi a Karamar Hukumar Dandume, inda suka kashe mutum daya a koina. Sun sace shanu sama da hamsin.

Majiyarmu ta kara da cewa an yi jana’izar su kamar yadda addinin musulunci ya tanada a garin na Bakkai a daren litinin. Kuma jami’an tsaro sun shigo garin, amma sun fita bada jimawa ba.

Shugaban Sojojin kasan Nijeriya, ya ce nan gaba kadan za’a murkushe yan bindigar nan, da suka addabi jihar Katsina dama arewa maso yamma. Ya Yi kira ga al’ummar da su ba jami’an tsaro hadin kai da kuma adduar samun nasarar kakkabe su.

Duk kokarin da wakilin mu ya yi na jin bakin kakakin Rundunar ‘yansanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isah abun ya ci tura.


Post a Comment

0 Comments

Close Menu