Mambobin kungiyar gwamnonin arewa sun yi taro a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni don duba yanayin rashin tsaro da ya addabi yankin.

Taron da aka yi ta yanar gizo wanda shugaban kungiyar gwamnonin, Simon Lalong ya jagoranta, ya jajanta a kan karuwar rashin tsaro a yankin arewa.

A yayin taron, gwamnonin sun fara zantawa a kan matakan da za’a dauka a kan rashin tsaron.

Daga cikin matakan, sun amince da kafa kwamitin kula da tsaro a arewa wanda zai dinga duba al’amuran tabbatar da tsaro a yankin.

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, shi aka nada shugaban kwamitin yayin da Gwamna Matawalle na jihar Zamfara da takwaransa na Gombe, Muhammad Yahaya suka zama mambobi.

Daya kwamitin ya samu shugabancin gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da gwamna Ahmadu Fintiri, Abubakar Bello da Aminu Tambuwal.

Sune za su tuntubi malaman addinai, sarakunan gargajiya da shugabannin yankuna a arewa.

Kamar yadda mai magana da yawun Gwamna Lalong ya sanar, kwamitin zai tabbatar da an saka bangarori da yawa wurin shawo kan matsalar tsaro a arewa.

Gwamnonin sun yanke hukuncin saka ‘yan banga, mafarauta da kuma kungiyoyin yankuna don tsara tsaron yankin tare da inganta rahotannin sirri.

A saboda haka suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba tsaron ECOWAS na barin shige da fice ta iyakokin kasar nan musamman a arewa.

A yayin jinjinawa gwamnatin tarayya a kan kokarin shawo kan matsalar tsaro, sun yi kira ga gwamnatin da ta inganta tare da tallafawa don kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga.

Sun amince da duba tsarin tattaunawa tare da amfani da tsarin dakarun soji wajen shawo kan kalubalen tsaro a yankin.

A kan hare-haren kwanan nan, gwamnonin sun jajantawa wadanda abun ya shafa, sun yi kira ga kungiyoyi da su kwantar da hankalinsu.

Sun tabbatar wa da mazauna yankin cewa kungiyar, gwamnatocin jihohi da na tarayya na kokarin shawo kan matsalar.