Daga Barrista Nuraddeen Isma'eel

Wannan fitatciyar Sanarwar tafito ne daga 'kungiyoyin wadansu zaratan matasa. Masu juni a jika, Wanda suke zaune acikin garin Zaria, Musamman cikin ganuwar Zaria.

Musabbabin Kafa ita wannan kwamiti, ko kuma muce 'kungiya na shirgan duk wani 'kato domin yana nuna soyayya ga gwamna El-rufa'i. Shine! Na 'Irin salon Mulkin da gwamna yake nunamawa a jahar kaduna na rashin sanin 'yancin Al'umma, tareda ya'ki da Addinai duk da fakewa da Cutar covid19.

Ita wanna 'kungiya, zata fara aiki nan bada jimawaba, kuma ga dukkan alamu suna nuni Cewa' 'kungiyar tana da tushe tare da kuma fitar da rassai a duk fadin unguwanni dake 'Karamar Hukumar Zaria.

Manufar 'yan Tafiyar wannan 'kungiyar shine' ya'ki da duk wani mai nuna goyon bayansa ga irin tsatstsauran matakan da gwamna El-rufa'i ya Kafa a Jahar Kaduna.

Wanda mabiya wannan 'kungiyar suka sanya mata suna da AJIBGI 'KATO.

Gare Ku masu Karatu' ko kuna goyon bayan Wadannan 'kungiyar ???