Aminu Badikko.
Kaduna Press.

Da Safiyar lahadi 21/07/2020, Dandalin Shuhada'u yankin (lmam Bakir) suka gudanar da taron karramawa ga darajojin hakkin shuhada, bayan bude taro da Addu'ah da Karatun Al-Qur'ani, da kuma Ziyarar Imam Hussain (As) sai a ka gabatar  Shugaban yankin/ (Zone) Prof Abdullahi Danladi, in da ya gabatar da jawabi na tunatar da "Yan'uwa game da  tallafawa lyalan Shahidai kamar yadda Sayyid Zakzaky (H) Yake da bukata da kuma kaiwa ga hadafin assasa shi Dandalin Shuhada'u din. 
Bayan kammalawar sa, sai Wakilin "Yan'uwa na garin Kaduna Malam Aliyu Tirmizy ya gabatar da jawabinsa me taken Karfafawa akan neman "Yancin Jagora (H), wanda Malamin yayi jawabinsa me cike da Shajja'awa tare da kira ga dukkan "Yan'uwa da mu mike tsaye wajen ganin Jagora Sheikh Zakzaky (H) yasamu "Yanci. Ya ce: shi kuma wannan fafutuka na kowa da kowa ne, ba a daukewa kowaba, kuma zamuyi tayine ba dare ba rana, har kaiwa ga hadafi na gaskiya, ya Kara jan hankalin mu akan tabbata akan fikirar Jagora (H) kyam, kada wani yayi wasa da lmanin ka wajen saka maka wata fikira da tayi hannun riga da ta Jagora (H).
In da a karshe a ka mika abu magana ga shugaban Mu'assasatus Shuhada Sheikh Abdulhamid Bello in da ya gabata da jawabin sa game da, halin da iyalan Shuhada ke ciki, tare da kara kira ga yan uwa da su daure wajen ganin sun sauke nauyin da ke kan su, game da iyalan Shuhada. Sannan an raba takar dun yabo ga wadan da suka shiga hakkin darajoji wajen tallafawa iyalan Shuhada. Sannan a kayi Addu'ah a ka tashi.