Daga Barrista Nuraddeen Isma'eel 

A Cewar Babban bankin 'kasa dake Abuja" 'kar'kashin Amincewar gwamnatin Tarayya! Ciki harda sanya hannun gwamnar Babban bankin. Mista Godwin emefiele" kan cewa!  za su cigaba da raba kudade ga Al'umma a matsayin bashi; anan gaba kasan, kamar yanda aka fara rarrabama wadansu ba'adin 'yan Najeriya a kwanakin baya da suka wuce.

Shidai wannan rabon kudin ta samo asali ne, sakamakon samun ma'kudan kudade da akayi daga Hannun wadansu attajiran Najeriya, kan ya'ki da Cutar koronabairos.

Duba ga yanda Al'umma aka tsare su a cikin gidajen su, babu Fita koda wurin aiki ne, da nufin su Kare Kansu daga ita wannan annobar ta korona, tare da bin dokokin hukumomin lafiya, kan hakane! gwamnatin Tarayya ta karkatar da Wadannan kudaden zuwa ga bankin 'kasa domin rabawa Al'umma bashi, don su 'kara samun Abin dogaro da kai.

Daga bisani a karo ta biyu. Sun 'kara bude fotel nasu, ta yanda aka samu miliyoyin Al'ummar da sukayi aflain, da nufin su samu Wadannan Kudaden da ake bayarwa daga Babban bankin 'kasa.

A 'karshe dai gwamnar Babban bankin Najeriya Godwin emefiele a inda yaci gaba da cewa' duk Wanda ya Tabbatar anbashi Wannan kudi' tofa! Dole ya Biya domin bashi ne aka bashi ba kyauta ba, sai yasa suke bu'katar VBM na mutum.

Sai dai ansamu wadansu Wadanda wurin aflain ta Neman bashin,  a karo ta biyu! basu bi 'ka'idoji kamar yanda ake bu'kataba kamar yanda na'urar su ta nuna masu.

A 'karshe dai wannan Rahoton ta samu ingantattun shedun gani da ido, kuma ma'aikata a babban bankin tarayyar dake Abuja. a yayin da gwamnatin Tarayya ta samu Shiga wata 'yar gajeruwar zama, da masu ruwa da tsaki kan rabama al'umma wadannan kudaden ta koronabairos a bisa bashi.