MUZAHARAR NEMAN GANIN AN SAKI SHEIKH ZAKZAKIY A KADUNA!!!
-KADUNA PRESS.

Dubun-Dubatar 'yan uwa Musulmi ne mabiya Jagora Sheikh Zakzakiy (H) suka fito domin kara jaddada kiransu ga hukumomin Nigeria akan su gaggauta sakin Jagora Sheikh Zakzakiy (H) ba tare da wani sharadi ba. kamar yadda babbar kotun da babban mai shari'a Mr. Kola wole ke jagoranta, mai mazauni a babban birnin tarayyar Nigeria Abuja ta bayar da umarni tun tsawon kusan fiye da shekaru uku da suka gabata.
An fara muzaharar ne da misalin karfe hudu dai-dai na rana, kuma an farota ne daga livintis round about aka hau kan titin Ahmadu Bello way aka gangara ta layin kano road aka rufeta a layin bayajidda street by kano road.

Andai fara kuma ankammala lami-lafiya ba tare da wani tashin hankali ba.
-KNPRSCD 06.
-27/07/2020.