Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi zargin cewa, ƙirƙirar cutar korona aka yi saboda kawai a haifar da tsoro da firgici a tsakanin mutane.

Furucin gwamnan ya zo ne a yayin da yake kara jaddada cewa, ba cutar korona ce ta yi sanadiyar mutuwar babban alkalin jiharsa ba, Mai Shari’a Nasir Ajana.

Gwamna Bello ya bayyana hakan ne a yayin zaman addu’ar sadakar uku na makokin marigayi Ajana da aka gudanar a ranar Talata.

Mai shari’a Ajana ya rasu ne a ranar Lahadi a wani asibiti cikin birnin Abuja.

Ya bayyana cutar korona a matsayin annoba mafi muni fiye da ta’addancin fashi da makami da na Boko Haram, yana mai bayyana takaicin cewa ƙirƙirarta kawai aka domin a yaudari ‘yan Najeriya.

Ya shawarci ‘yan Najeriya a kan kada su fada cikin tsoro ko wani sharri kan batun cutar korona, ya na mai cewa, “cuta ce da aka shigo da ita, ana yada ta da muzgunawa mutane ba gaira babu dalili”.

Ya yi nuni da cewa babu abin da ke saurin kashe mutane fiye da tsoro da firgici, yana mai kira ga mutane a kan kada su yarda cutar ta yi mummunan tasiri a kansu.