Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Free Sheik Zakzakiy A Kaduna

MUZAHARAR NEMAN A SAKI SHEIKH ZAKZAKIY A KADUNA...!!!
-KADUNA PRESS

Dubun-Dubatar 'yan uwa Musulmi ne mabiya Jagora Sheikh Zakzakiy (H) suka fito domin kara jaddada kiransu ga hukumomin Nigeria akan su gaggauta sakin Jagora (H) ba tare da wani sharadi ba kamar yadda wata babbar kotun da babban mai shari'a Mr. Kola wole ke jagoranta, mai mazauni a babban birnin tarayyar Nigeria Abuja ta bayar da umarni tun tsawon kusan fiye da shekaru uku da suka gabata.
Kamun Shehin malamin ya biyo bayan harin da jami'an tsaron Nigeria suka kai masa a mazauninsa dake gyallesu a cikin garin Zaria dake jihad kadunan Nigeria,
Bisa fakewa da sukayi da dalili mara tushe da rashin makama na cewa wai mabiya Shehin ne suka tarewa tawagar hafsan-hafsoshin sojin Nigeria Gen. T.Y Buratai da nufin yi masa kwantan bauna a dai-dai filin polo dake daura da muhallin Husainiyya Baqiyyatullah dake G.R.A Zaria.
Sedai 'yan uwa musulmi Maya Shehin Malamin sun musanta zargin ta yadda suka kayar da hukumomin tsaron da gwamnatin tarayya a gaban kutun ta Mr. Kolawale.
An fara muzaharar ne da misalin karfe hudu dai-dai na yamma, kuma an farota ne daga livintis round about aka biyo titin Ahmadu Bello way aka shiga layin kano road aka rufe muzaharar a bayajidda street by kano road.

Andai fara kuma ankammala lami-lafiya ba tare da wani tashin hankali ba.
-KNPRSCD 06.
-11/07/2020.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu