Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Shugaba Buhari Zaije Mali


SHUGABA BUHARI ZAI ZIYARCI KASAR MALI...!!!
-KADUNA PRESS.
A ranar alhamis din gobe 23/07/2020. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi Bamako babban birnin ƙasar Mali.

Tafiyar tasa ta biyo bayan tattaunawarsa da Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda yana daga cikin masu shiga tsakani daga ƙunigyar ECOWAS da suka je Mali domin kawo sasanci.

Wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Yammacin Afrika kamar su Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou sun amince su hadu a Mali domin tattaunawa don kawo sasanci tsakanin Shugaban Mali Boubacar Keita da kuma 'yan adawa a ƙasar.

Ana sa ran Shugaban Ghana Nana Akufo Addo da kuma na Cote d'Ivoire Alassane Ouattara za su halarci tattaunawar.
-KNPRSCD 06.
-22/07/2020.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu