Daga Barrista Nuraddeen Isma'eel

Ministan kudi da tsare-tsaren bajet a Najeriya hajiya zainab Ahmed, ta 'kara da Cewa' 'kasashe sama da 5 ne suke bin Najeriya makudan bashin kudade.

Ministan taci gaba da Cewa' Zamu fara Biyan Wadannan kudadenne domin ragewa Najeriya nauyin dake kanta, don gujema Shiga jin kunya a nan gaba.

Sanin kowane Najeriya ta ciyo basuka masu 'Dimnbin yawa domin aiwatar da Wadansu mihimman aiyuka, inda muka samu Yardar bankin duniya dake 'kasar caina ta mara mana baya na wurin yarda da ciwo bashi, a duk 'kasar da muka ga Dama.

Hakan yasa ba zamuyi 'kasa a gwiwaba sam' don fara rage basukan dake kan mu, domin cika Al'amari bisa 'ka'idojin da akayi a Tsakani.

Za'a fara biyan Wadannan kudaden ne a 'karshen Wannan watan ta July da muke ciki.

Ministan tayi Wannan bayaninne a wata ganawa da tayi tare da masu ruwa da Tsaki kan harkokin ciwo bashi na duniya dana Najeriya, da masu hannun jari a gwamnati a makon data gabata a Abuja.