A yau lahadi 20 ga watan Zulhijja 1441 wanda yayi daidai da 9 ga watan Augusta 2020 ne yan'uwa Almajiran Sheikh Ibrahim Yaqoub El Zakzaky na da'irar Kaduna suka gabatar ma taron Edil Ghadeer.

  Taron wanda ya gabata a Kadu

na yasamu halartar daruruwan yan'uwa tare da samun albarkar halattar Malaman mu Ali,Ali har su uku(Malam Aliyu Tirmizy,Malam Aliyu Kwana tare da Malam Aliyu bakin ruwa)

   An bude taron da add

u'a sai aka gabatar da karatun Alqur'ani mai girma sannan sai mawaka sukayi baje kolin baitoci ga Shugaban mumunai Imam Ali(AS).

   Malam Aliyu Kwana shine wanda ya gabatar da gwala gwalan jawabai a wurin taron.A cikin jawabinsa ya gabatar da ayoyi da hadisai akan khalifancin Amirul Mu'umin

Imam Ali (AS).Sannan kuma yayi albishir ga yan'uwa ma'abota wilayah cewa duk wanda ya samu da wilayar Ahlul bayt to yayi godiya ga Allah domin kuwa za'a tambaya duk
wanda ya bar duniya akan wilayar Imam Ali (AS).Daga karshe yayi kira ga yan'uwa da cewa dole ne duk wanda samu kansa da wilayar Amirul mumunin to Sayyed Zakzaky
na binsa bashin shiriya da saninsa,dole ne kayi inkari akan zaluncin da akewa Sheikh Ibrahim Yaqoub El Zakzaky domin kuwa duk wanda ya nusar da kai hanyar Ahlul bayt wani irin tukuici ne zaka masa.

   Sai wakilin yan'uwa na Da'irar Kaduna Malam Aliyu Tirmizy ya gabatar da nasa jawabin.A cikin jawabinsa ya kawo wani kissa akan am tambaya Imam Mahdi(AS) akan meyasa mutane bazasu zabi

shugabansu da kansu ba sai Imam Mahdi (AS) yace ay mutane basusan maslahar kansu ba.sannan ya kara da cewa Manzo (S) yace mubarazar Imam Ali(AS) da Amru yayi daidai da ibadar dukkan muminai mutum da aljan. A karshe yayi kira ga yan'uwa  su kara jajircewa akan fafutuka wajen ganin wannan azzalumar Gwamnati ta sako Sheikh Ibrahim Ya'qoub Elzakzaky.

   Daga karshe an raba kyaututtuka ga

yara masu suna Ali da kuma Fadima sai Malam Aliyu bakin ruwa ya rufe taron da addu'a.


             


Fatima Muhammad Ahmad

Kaduna press