A safiyar Yau Monday 31/8/2020  da misalin karfe tara 9:00am na safe a ka yi janaizar Dan uwa abokin aiki shahid Bashir Muhammad, wanda jami'an tsaron yan sanda  suka shahadan tar da shi, a yayin harin ta'addanci da suka kaiwa masu jerin gwanon ashura Dan tinawa da kashe jikan Manzon Allah (S) wanda a ka gudanar a jiya Lahadi a cikin garin kaduna.
An gudanar da sallah tare da janaizar a shahid Muhammad Bashir kd Press  a Darur Rahama dake danbo cikin garin zariya, Shugaban Mu'assasattu Shuhada sheikh Abdulhamid Bello shi ne ya jagoranci yi masa janaiza. Muna fatan Allah ya amshi shahadar sa, ya tsinewa makasan mu.
Hakika shahid bashir ya kasance yana daga cikin yan media na kd press mai kokarin gaske Shahid ba shi da Abokin fada ko kadan, kowa nashi ne, muna fatan Allah ya tashe shi a cikin shahidan Karbala tare da imam Hussain (as).  
Ga wasu daga cikin hotunan da muka dauko muku a wajan Jana'izar 

Kaduna press 
31/8/2020