Kamar kowace Shekara, cikin yarjewar Allah (T),  yau laraba 05/08/2020, "Yan'uwa Musulmi  Almajiran Sheikh lbraheem Yakub Al-Zakzaky (H), na yankin kaduna da kewaye suka gabatar na goron Sallah ga lyalan Shahidai. 
Taron ya gudana ne cikin temakon Allah (T), tare da bude taro da addu'a, Karatun Al'kur'ani yabiyo baya, sai wake me taken jinjina ga Shahidai da ya gabata a harshen mawakan gwagwarmaya tare da jagorancin Hadimin lmam Hussain (as), Auwal K/Mashi, sannan Jawabin makasudin taro ya gabata daga bakin wakilin Mu'assatus shuhada na Kaduna Ml.Aminu Unguwar rimi Allah ya kara masa juriya da hakuri. 
Taron ya samu tagomashin jawabai daga  Manyan Malaman Mu, Me jawabi na farko shine Sayyida Aliyu B/ruwa, wanda ya jawo hankula akan wulaya da mujahada da dan faruwa ga Allah wanda zai kaimu zuwa ga samun rabo irin na "Yan'uwan da suka gabacemu (Shuhada'u). 
Sai mai jawabi na biyu, wakilin "Yan'uwa na halkar lmamul Hujja (A.T.F) Ml Auwal Shu'aib H/rigasa, wannan ya albarkaci mahallin da jawabansa me taken farkarwa ga lyalan Shuhada wajen tsayuwa da kansu ta hanyar yin sana'a da samun kwarewa akan sana'oi daban daban, tare da kula da lyalan da aka barmasu wajen ganin tarbiyarsu ta inganta daidai gwargwadon iyawar su, 
Sai Mai jawabi ta Uku Malama Jamila Auwal Mukhtar Sahabi ce ta kara albarkar majalisin da gwalagwalan zantukanta me Shajja'a lyalan Shuhada'u akan su zama masu Kame kai da izza da karamci, su san cewa su ba makaskanta bane, su mutanene masu mutumtaka da alfarma a Duniya da Lahira, tare da juriwa ga dukkan matsalolin da ya bijoro garesu da maida lamarinsu ga Allah (T). 
Sai me Jawabi na karshe, Wakilin "Yan'uwa na Kaduna Ml Aliyu Tirmizy ya kammala taron da nashi Jawabin, ya fara da barka da Sallah, tare da aran bakin "Yan'uwa wajen ba su lyalan Shahidan hakuri na rashin yin abinda ya kamata ga "Yan'uwa,  kodai sabida matsalolin rayuwa na yau da kullun da aka tsinci kai aciki, ko kuma dai rauni namu "Yan'uwa din, sannan yaci gaba da jawaninsa kamar yadda ya saba a irin wannan munasabobin wanda ya shafi "Yan'uwa ne kawai, kuma sun sabaji daga bakinsa me albarja a irin wannan taro na lyalan Shahidai me albarka, jawaban yana da Mallin fadinsa, daga karshe ya karkata ga su lyalan Shahidai din, tare da basu shawarar yadda zasu tsayu da kawunan ta hanyan sana'oi da zai basu daman su tsayu da kan su ba tare da jiran akawo masu ba, ya karkare da bada shawara ga su wakilan Shuhada dana Unguwa, wajen ganin ansamarma da lyalan Shahidan sana'a musamman "Ya"yansu, sabida tsayuwa da kai. 
Aka raba kyaututtuka ga lyalan Shahidan aka Ci ala Sha daidai gwargwado akayi addua aka tashi. 
Alhmdlh.