Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

IMAM HUSSAIN DA WAKI'AR KARBALA

 


```Fatima Muhammad Ahmad✍🏼```
Kaduna Press

وَلا تَحْسَبَنَّ الَّذِينَ قُتِلُوا فِي سَبيلِ اللهِ أَمْواتًا بَلْ أحْياءُ عندَ رَبِّهِمْ بُرْزَقُونَ

"Kada ka yi zaton wadanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A'a, rayayyu ne su, a wurin Ubangijinsu. Ana ciyar da su".

(Suratu Al'Imrana: 3:169)

Hakika Imam Husaini bn Ali (a.s) ya kasance wata alama ce, makaranta sannan kuma wani yunkuri na siyasa da addini tilo cikin tarihin Musulunci. Don haka ne rawar da ya taka ta kasance mai girma haka nan kuma tasirinsa.... Shi ya kasance wani karfi ne mai motsa al'amurra cikin tarihin Musulunci, musamman ma a bangaren Jihadi a tafarkin Allah. Wannan yunkuri na Imam Husaini (a.s) dai ya kasance raye duk cikin shekaru da karnoni, wanda kuma yake da gagarumin tasiri cikin zuciyar al'umma da kuma wayewarsu.

Akwai dai wasu dalilai na siyasa, zamantakewa da addini da suka sa Imam Husaini (a.s) ya mike tsaye don fuskantar Yazid bn Mu'awiyya da mulkinsa na zalunci da ashararanci. Mafi girma daga cikin wadannan dalilai dai shi ne yin hawan kawara ga jiga-jigan da shari'ar Musulunci ya dogara a kansu da Yazid din ya yi a lokacin mulkinsa. Daga cikin manyan jiga-jiga da akidun da Imam Husaini (a.s) din ya so rayawa a wannan lokaci su ne:

1- Girmama ra'ayuyyukan sauran al'umma da kuma tuntubarsu cikin harkokin gudanar da mulki.

( ...وَشَاوِرْهُمْ في الامْرِ.... ) "...Kuma ka shawarce su cikin al'amurra..." (Suratu Al' Imrana: 3:159)

2- Dokoki da hukumce-hukumce su kasance sama da kowa. Don kuwa su ne jigo wadanda shugaba zai yi aiki da su, wajen gudanar da mulki da kare hakkokin al'umma.

( فَاحكُمْ بين النَّاسِ بِالْحَقِّ ولاَ تَتَّبِع الهوى... ) "To, ka yi hukumci tsakanin mutane da gaskiya, kuma kada ka biye wa son zuciya…". (Suratu Sad: 38: 26)

( فَاحكُمْ بينهُمْ بمَا أنْزَلَ اللهُ ) "…Sai ka yi hukumci a tsakaninsu da abin da Allah Ya saukar…." (Suratul Ma'ida: 5:48)

3- Tabbatar da adalci da daidaituwa tsakanin dukkan al'umma, ba tare da la'akari da kabila ko kuma inda suka fito ba.

( انَّ اللهَ يأْمُرُكُمْ أنْ تؤَدُّاالأمَانَاتِ الى أهْلِهَا واِذاحكَمْتُمْ بين النَاسِ أَنْ تحكُموا بالعدلِ ) "Lalle ne Allah Yana umurtanku da ku bayar da amanoni zuwa ga masu su. Kuma idan kun yi hukumci a tsakanin mutane, ku yi hukumci da adalci...". (Suratun Nisa': 4:58)

4- Tabbatar da cewa shugaba ya kasance mai tsoron Allah kana kuma kwararre don ya samu daman duganar da aikinsa yadda ya dace.

Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa:

"An umarcemu da mu ajiye mutane a matsayin da yayi daidai da su".

5- Tabbatar da cewa an raba dukiyan al'umma daidai wa daida:

ما أَفاء الله على رَسُولِهِ منْ أهْلِ القُرى فَلِلَّهِ وَلِلرَّسولِ وَلذي الْقُربى والْيَتامى والمَساكِين وابنِ السَّبيل كَيْ لايَكونَ دولةً بين الأغْنياءِ منكُمْ وما اتَاكمُ الرَّسولُ فَخُذوهُ ومَا نهَاكُمْ عنهُ فانْتَهوا واتَّقوا اللهَ إِنَّ اللهَ شَديدُ العِقَابِ

"Abin da Allah Ya sanya shi ganima ga ManzonSa daga mutanen kauyukan nan, to, na, Allah ne, kuma na ManzonSa ne, kuma na masu dangantaka da maraya da miskinai da dan hanya (matafiyi) ne, domin kada ya kasance abin shawagi a tsakanin mawadata daga cikinku, kuma abin da Manzo ya ba ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da takawa. Lalle Allah, Mai tsananin ukuba ne". (Suratul Hashr: 59:7)

An ruwaito Imam Ali (a.s) yana cewa:

"Da a ce (dukkan abin da ke cikin wannan duniya) nawa ne, to da na raba shi daidai wa daida tsakanin mabukata da matalauta. To ya ya lamarin zai kasance a lokacin da wadannan abubuwa suka kasance kayan Allah ne".

6- Hakkin yin suka, ba da shawara da kuma tattaunawa kan yanayin gudanar da mulkin shugaba.

) ولْتَكُنْ منكُمْ أمَّةٌ يدْعونَ الى الخَيرِ ويأْمرونَ بالمعروفِ وينْهونَ عنِ المنكَرِ وأولئكَ هُمُ المُفْلحونَ (

"Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umurni da alheri, kuma suna hani daga abin da ake ki. Kuma wadannan, su ne masu cin nasara". (Suratu Al' Imrana: 3:104).

Manzon Allah (s.a.w.a) yana cewa:

"Mafi girman jihadi shi ne fadin gaskiya a gaban ja'irin shugaba".

Hakika Imam Husaini (a.s) dai ya ga yadda lamarin siyasa da zamantakewar al'umma suka lalace, kana kuma yadda ake gudanar da mulki sam-sam ya saba wa tsarin Musulunci, face ma dai kokari yake ya tunbuke tushen Musuluncin. Ya kasance yana sane da yadda al'umma suke fuskantar wahalhalu da bala'oi daban-daban daga masu mulkin wancan lokacin, don haka ya ke son ya gudanar da abin da ya hau kansa na addini wajen kawar da irin wannan yanayi da kuma dawo da martabar Musulunci.

Don haka ne ya mike tsaye don yi bore, wannan bore da ke cike da darussa da kuma dabi'u na kwarai. Imam Husaini (a.s) ya sadaukar da ransa, dukiya da iyalansa don kalubalantar zalunci da babakere. Ya yi hakurin jurewa duk wahalhalun tafiyar darurrukan kilomitoci dare da rana don cimma wannan manufa wacce ta zo a daidai lokacin da ta dace, a takaice dai ya kuduri aniyar sadaukar da kansa ne gaba daya.

Daga karshe dai an kashe shi tare da 'ya'yayensa, iyalai da kuma sahabbansa, aka lalata jikkunansu masu tsarki da kuma daukan kawunansu daga Karbala zuwa Kufa daga karshe kuma aka wuce da su Damaskus. Haka nan kuma aka kame matayen da suka kasance tare da shi a matsayin fursunonin yaki cikin tsananin zafin hamada. Tun farko dai Imam Husain (a.s) ya san hakan zai faru to amma ko da wasa bai yi tunanin mika wuya da kuma janyewa daga wannan kuduri nasa ba.

Shakka babu, wannan yunkuri da mafi girma da daukaka mutanen wancan lokacin ya jagoranta, zai kasance mafi girman yunkuri a fagen kyawawan dabi'u da kuma halaye na addini.

To saboda wannan dalili ne ya sa muka gabatar wa mai karatu wannan takaitacce bayani amma wanda yake cike da muhimman al'amurra, dangane wannan yunkuri na Imam Husaini (a.s) wanda yake da muhimmancin gaske wajen tabbatar da Musulunci wanda kuma ya cika littattafan tarihi.

Mun yi amanna da cewa dole ne a yi darasi dangane da wannan yunkuri, don fahimtarsa da kuma daukan darussa daga gare shi ga duk wani wanda yake son bin sahunsa da kuma fada da azzaluman sarakuna.

Muna rokon Allah, Madaukakin Sarki, da Ya sanya wannan aiki abin amfanuwa ga masu karatu da kuma jan hannayensu zuwa ga shiriya. Don Shi Mai sauraro ne kuma Mai amsa addu'a.

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa Barakatuhu

Post a Comment

0 Comments

Close Menu