MUZAHARAR NEMAN GANIN AN SAKI SHEIKH ZAKZAKIY A KADUNA!!!-KADUNA PRESS.

Dubun-Dubatar 'yan uwa Musulmi ne mabiya Jagora Sheikh Zakzakiy (H) suka fito domin kara jaddada kiransu ga hukumomin Nigeria akan su gaggauta sakin Jagora Sheikh Zakzakiy (H) ba tare da wani sharadi ba. kamar yadda babbar kotun da babban mai shari'a Mr. Kola wole ke jagoranta, mai mazauni a babban birnin tarayyar Nigeria Abuja ta bayar da umarni tun tsawon kusan fiye da shekaru uku da suka gabata.
Masu muzaharar suna rike da hotuna masu dauke da Sheikh Zakzakiy, da mazlumiyar da akayi masa, kana suna tafe suna rera take kala-kala na bukatar ganin gwamnati ta saki Jagora (H) ba visa ka'ida ba.
An fara muzaharar ne da misalin karfe shida na gamma, kuma an farota ne daga kabala junction aka hau kan titin express way dake hanyar Abuja to Zaria, kuma an rufetane a kagoro by express way junction.

Andai fara kuma ankammala lami-lafiya ba tare da wani tashin hankali ba.
-KNPRSCD 06.
-17/08/2020.