JAMI'AN TSARO SUN KASHE DAN SHI'A A KADUNA YAU LAHADI...

-KADUNA PRESS.

A yau lahadi 30/08/2020, 11/01/1442, 'yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzakiy na da'irar Kaduna sunbi sahun takwarorinsu na sauran garuruwa da yankuna domin gabatar da muzaharar Ashura na tunawa da waqi'ar data faru da jikan Manzon Allah Imam Hussaini a filin Karbala, tun a karni na farko bayan wafatin Kakansa Manzon Allah (S), kamar yadda suka saba suna fita a duk ranar goma sha daya ga watan muharram.

Da misalin karfe uku saura kusan mintuna bakwai na yamma ne 'yan uwan sukayi kabbara domin fara muzaharar, kabbararsu ke da wuya jami'an tsaron suka bude musu wuta sukayi musu harbin kan mai-uwa-dawabi, suna harbi ta ko wanne bangare.

Haka aka cigaba da muzaharar nan har saida takai gabda liventis round about sannan aka rufe ta.

A ta daya bangaren kuwa ansamu wasu baradan matasa ne suka rike jami'an tsaron ta wajen hanasu sakat, suka dakile harbin da suke yowa cikin 'yan uwan suka hanasu sakat, suna kabbarori suna kiran sunayen ismullahil azeem domin neman samun sabatiy daga Allah.

Matasan basu gushe ba har saida suka tabbatar harsasan jami'an tsaron sun kare, sun juya da mugun gudu sun tsere, sannan suka dawo sukayi tasu muzaharar bayan ta farkon ta tashi.

Sedai a yayin harbin nasu jami'an tsaron sun shahadantar mana da babban jigo, dan uwa abokin aiki, ma'aikacin Kaduna Press wato Malam Bash (Bashir Muhammad U/ma'azu).

Zuwa hada wannan rahoton munada tabbacin anharbin akalla mutum hudu sannan kuma ma'aikacin mu Mal. Bash shine kadai wanda yayi shahada.

-KNPRSCD 06.

-11/01/1442.

-30/08/2020.