Watan Muharram wata ne da adalci ya tunkari zalunci kuma gaskiya ta kalubalanci karya kuma tabbatar da cewa a ko da yaushe a tarihi gaskiya na rinjayar karya.

Muharram wata ne wanda Musulunci ya sake rayuwa ta hannun Shugaban dukkan mujahidai (Imam Husain) kuma aka tserar da shi daga makircin banu Umayya lalatattu wadanda suka kai addinin Musulunci ga halaka.

Jinin Shugaban Shahidai (Imam Husainin) ne yake haifar da yunkuri a cikin jinin jama’ar Musulmi.

A mazhabar Shi’a, Muharram wata ne wanda a cikinsa aka ci nasara da jini da kuma sadaukar da kai.

Muharram watan babban yunkurin Shugaban Shahidai ne na farin cikin waliyan Allah wanda ta hanyar yunkurinsa na tinkarar Dagutu, ya karantar da Bil Adama yadda ake ginuwa a yi tsayuwar daka da kuma cewa hanyar rusa azzalumai da karya ma’abuta mulkin kama karya ita ce sadaukarwa. Wannan kuwa ita ce babbar karantarwar Musulunci ga dukkan al’ummomi har zuwa karshen zamani.

Lokacin yunkuri da jaruntaka da sadaukar da kai na  farawa ne da shigowar watan Muharram. Wata ne wanda jini ya yi galaba a kan takobi. Wata ne da karfin gaskiya ya wargaza na karya, ta kifar da karya har abada a bakin dagar azzalumai da hukumomin Shaidan. Wata ne wanda ya karantar wa al’ummomi masu zuwa gaba a dukkan tsawon tarihi, yadda ake galaba a kan masu, wata ne wanda a cikinsa ne galaba gaskiya a kan manyan masu karfi. Wata ne wanda Imamin Musulmi ya karantar da mu hanyar tunkarar ja’irai a duk tsawon tarihi.

Sun kashe Shugaban Shahidai tare da mabiyansa da danginsa, amma sakonsa ya isa zuwa gaba.

Shahadar mai martaba Imam Husain (a.s) ta rayar da akidar Musulunci.

Rayar da bukin Ashura (goma ga watan Muharram lokacin da Imam Husaini ya yi shahada), na da muhimmanci a al’amurran ibada da siyasa.

Juyin Musulunci na Iran ci gaba ne daga yunkurin Ashura kuma babban juyi ne na Ubangiji wanda ya bubbugo daga gare Shi.

Gwabzawar Karbala ta ruguza fadar azzalumai da jini, mu kuma Karbalarmu ta rusa fadar shedana ce.

Ku raya Karbala da sunan Suhgaban Shahidai mai tsarki, domin rayar da su na tabbatar da rayar da Musulunci.

Al’amarin Karbala wanda siyasa ke kan gaba a cikinsa, lalle ne a raya shi.

Wajibi ne ga jama’ar al’ummarmu da su raya al’amarin Ashura a bisa yadda Musulunci ya tsara tare da dukkan hallara.

Ku kula da watan Muharram, domin dukkan abubuwa da muke da su daga gare shi ne.

Watan Muharram da Safar su ne suka raya Musulunci.

Duk wannan hadewar kalma guda din wanda shi ne asasin cin nasararmu, ya samo asali ne daga albarkacin zaman makoki da tarurrukan juyayi da kuma wa’azce-wa’azcen da yada Musulunci.

A yi kokarin ganin an yi taron makoki da zaman juyayi domin tunawa da Shahadar Salihan Bayi, Farin Cikin Raunana (Imam Husaini (a.s) ), tare da cikowar yawan jama’a da kuzari mai yawa, domin wadannan bukunna suna ishara ne ga ranar cin nasarar hankali a kan jahilci, adalci a kan zalunci, amana a kan ha’inci da kuma hukumcin Musulunci a kan na Dagutu. A daga tutocin Ashura da ke shafe da jini a matsayin ishara ga isowar ranar ramuwar gayyar wadanda aka zalunta a kan azzalumai.

Muharram wata ne, wanda mutane a cikinsa a shirye suke su saurari gaskiya.

Yin kuka domin bakin ciki wa Imam Husaini (a.s) da rayar da yunkurin da tabbatar da gaskiyar cewa mutane marasa yawa sun tunkari babban azzalumin sarki, dukkan haka suna a matsayin abubuwan da ke wanzuwa a yau.

Dukan kirji a jerin gwano, dole ne ya zama yana da ma’auni.

Ashura rana ce ta zaman makokin al’ummar da aka zalunta, ranar sake haifar da Musulunci da  Musulmai.

____________
 
Bani Umayya sunan wata gidan sarauta ce wadda suka hau karagar shugabancin al’umman Musulmi a shekara ta 40 bayan hijira (662 A.D) bayan halifofin nan guda hudu, har zuwa shekara ta 132 bayan hijira (750 A.D). Shugaban wannan masarauta shi ne Mu’awiyya ibn Abu Sufyan, wanda ya assasa wannan mulki na kama karya wanda a fili ya saba wa koyarwa ta Musulunci. Hakika tarihi ya shaida irin zalunci da babakeren da ya faru a duniyar musulmi lokacin mulkin Banu Umayya, kamar su kisan gilla, bacewa, tsare mabiya Ahlulbaiti a cikin fursunoni da kuma kashe Imam Husaini (a.s) da mabiya Yazid ibn Mu’awiyya suka yi