Yarone mai kokarin gaske ranar Muzaharan tare muke aiki a Gida sai yacemun baba lokaci yayi fa sai nace mai bari mukara wanan wajan sai mutafi, can yakara cewa baba kada muyi latti, sai na wanke jikina muka kama hanya. 

Zuwan mu wajjan keda wuya sai yan sanda suka tare mu ba hanya sabo da sunfara harbi mukuma muna tsakiyansu suna harbin masu muzahara, muna binsu a baya sai shaheed Muhammad Sani yace mun baba kabi gefe muka wuce can wajan yan uwa, sai na ce mai to bayan munyi gaba sai suka kara bude wuta da harbi nasha zasu samaini a bayana sabo da harbi kawai suke ba kaukautawa sai naji shaheed ya dira akan mashin din rabuwana ke nan da shi, yace mun baba kayi gaba tunda kana da mashin kasamu wuri katsaya sabo da daukan wanda a ka  harba sai can naga an harbi mutun biyu an wuce dasu bayan nan sai natashi nayi gaba  ban sake  ganinshi ba sai dai naji waya ance mun an harbeshi .waje biyu .da kirjinsa biyu sai bayan sa .
Munyi kokarin kaishi asibiti bayan ankawoshi  Gida sai mukasaurara sabo da yanayi dakuma kai Kawo da Jammi.an tsaro kayi a ranan .
Amma cikin yardan Allah muna kaishi asibiti akayimai aiki kuma alhamdulillah ansaamu nasara.
Bayan nan shahid Muhammad Sani yayi takokarin yatashi sabo da har bayan anyimai aiki  akwai karfi a jikinsa.
Nacemai kayi hakuri kazauna yace baba nasamu sauki gobe ma Gida zani sai nacemai Gida kuma yace eh.
Bayan mungama fira nabarsu dashi damai jinyannsa.
Yacemun baba kacema ummata suyafemun da abokaina gashi badaman  suzo ganina sabo da asibitin ba a barin zuwa dubiya.
Nadawo Gida kenan nayima yan uwana busharan cewa anyi aiki kuma jiki yayi kyau alhamdulillah ansamu nasara. 
Nakoma na Dan kishingida sabo da gajiya gashi kuma kusan kwana biyu bansamu nayi bacci ba.
Can Sai naji kiran waya ina dubawa sai naga mai jinyan sane .
Yacemun Sai dai muyi hakuri Muhammad Sani yayi shahada.

Innalillahi wa inna illahil rajiun,
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AMINCIN ALLAH GAREKA YA SHAHEED MUHAMMAD SANI. RANAN HAIFANKA DA RANAN TASHINKA KANA MAZLUM,

Kaduna press
KNPRSCD 005.
07/9/2020