– Shaikh Ibrahim Zakzaky (H). 

Kaduna press ✍ 
©17/09/2020

“Bamu da wani uzuri, sabida haka abinda yafi alkhairih garemu shine mu taru gaba ɗayanmu muyi magana da kalma ɗaya. Mu musulmine! Kuma musulumci shine addininmu, kuma dashi ne zamuyi aiki wajan gudanar da rayuwarmu. Waya isa ya hana? Babu. Amma mutane suna cewa bamu da ƙarfi. Ko suma sukan ce ‘sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi’ kuma balantana ma mu muna da garanti daga wajan Allah cewa nasara tamu ce. Muce hakane ɗin wani yace ba zai yiwu ba mana! In yasa yayi mana ruwan bama-bamai, ƙarshen al’amarin kuma dole sai addinin Allah ɗin ya tabbata. 

“Hujjarsu ƙarfi, hujjarmu Gaskiya. Muna da Allah basu da Shi, Afwan Malam, saboda Allah meye naka na tsoro. Duk wani makyarkyata da wani jin cewa ai abinne sai anbi a hankali, da anyi wani ɗan wayo-wayo, kunsan yadda duniyar ta ɗan sake, yanzu bamu da ƴan boko sosai, kuma gashi-gashi... Duk wannan zancen kawai ne, duk ba da waɗannan ne ake yaƙi ba, ana yaƙi ne da Imani. Idan mu riƙe addini shikenan. Falillahil-Hamd, Allah Na tare damu. 

“Allah Ta'ala na farko har yana ƙarfafa musu gwiwa da cewa, akwai Mala’iku zasu taimaka musu. Yace; wannan kuma dundai zuwa yai ƙarfi ne, zuciya tayi ƙarfi, amma Allah yana bukatar wasu Mala’ikune domin Ya tarwatsa rundunar shaiɗan? A'a, duk yadda yaso ya juya rundunar shaiɗan sai yayi. Mu gwadamu akeyi, indai mun bi gwaji Falillahil-Hamdu, sai nasara. 

“Sabida haka zan ƙarƙare maganarnan da cewa; makomar ƙasarnan, anƙi ko anso Addinin Musulumci ne! Shi zai dawo yayi iko damu, kamar yadda yayi iko da na farko. Wannan ba zai zo ne kawai, sakaka ba, kamar yau ana Lahadi gobe a wayi gari kawai ace jiya kaga ba addini ake ba, yanzu an dawo addini. Kuma ba zai zo ta hanyar fir'aunoninmu ba! Ta yiwu kuce mai yasa nake ce musu fir'auna, fir'auna shine wanda baya bin Allah a sha'anin mulkinsa. Koda ko yace shi musulmi ne. To addinin ba zai fito mana ta fir'aunoninmu ba, al’ummar musulmi ne zasu tashi su kawar da fir'aunoni. Kuma dole sai an fafata, wannan ba wani makawa sai dai kar kuji tsoron fafatawar domin akwai garantin nasara.

“Ya rage ma mutum, la'alla ko zai ce wannan hakane ya bada tasa gudummawar ayi dashi, ko kuwa zai yi guna-guni ya koma baya. Don wani lokaci idan mu kai magana mutum yaji magana ta fita fess! Sai yace 'Aha' abinda ma shi mai maganar ɗan kaza ne, wai ya rusa maganar kenan. Ƙaryarka! Kace ko ɗan menene, hanya ce ta Allah kwara ɗaya rak! Ba guda biyu ne ba, kuma Alhamdulillah daman an kama hanya, ya ragema mutum ya zaɓi na zaɓa, ko yazo ayi dashi, ko kuma ayi babu shi. Amma za a yi. Idan mutum yazo ayi dashi ya taimaki kansa duniyarsa da lahirarsa, idan bai zo anyi da shi ba, za a yi kuma ya cuci kansa duniyarsa da lahirarsa. 

“In abun naba mutum shawara ne, sai nace; yi tunanin wace gudummawa zaka bayar, kai a kankin kanka, ka fara da wannan, nemi ilimin addinin musulumci, siffanta da rayuwa ta musulmi a rayuwarka, sannan bada gudummawarka wajan tabbatar addini, kuma Insha Allahu addinin zai tabbata”. 

- Wani yanki daga cikin Jawabin Sayyid Ibrahim Zakzaky(h) daya gabatar akan Tabbatar da Addinin Musulumci.

Kaduna press ✍ 
©17/09/2020