*KYAKYAWAN AIKI DAGA ZANTUKAN AHLUBAITY(as)* 

By
*Kaduna press* ✍🏻

Bismillahi Rahmani Rahim 
Allahuma salli Ala Muhammmad wa ahlai muhammad 

Ya kai dan uwa mai daraja wani aiki kakeyi domin gani ka aikata aiki mai kyau domin koyi da Gidan Manzon Allah (saw) shin ko kasan an ruwaito daga 
Imam Ali (As) yake cewa ga ƴaƴansa Imam Hassan da  Hussain (as) a maganarsa bayan Ibn Muljam ya sareshi, "Kada ku taɓa barin aikata kyawawan aiki da ƙauracewa munana, kuma kada ku bari shaidanu suyi galaba akanku, domin in hakan ya faru, zaku kira Allah amma bazai amsa muku ba" wannan idan ka duba cikin Nahjul Balaga, Wasiƙa ta 47. 

Haka kuma an samo daga 
-Manzon Allah (S) yace, "Duk wanda yaga ana aikata mummunan aiki, yayi ƙoƙarin hanawa da hannunsa, idan bai samu damar hakan ba ya hanna da halshensa, in hakanma bai samu ba yaƙi abin a zuciyarsa, hakan shine matakin ƙarshe ga mafi raunin Imani" Al-Targib wal Tarhib, Mj 3, Sh 223.

-Ƴan uwa muzam masu aiki da kywawan aiki da hani ga munana a karan kanmu da wasunmu. Allah ya datar damu 

*daga Taskan kyakyawan aiki daga ✍🏻 Kaduna Press*