Daga Muhammad Bin Hamran daga Abu Abdullah (AS) yace 

Duk wanda yace La ilaha illallahu da ikhlasi zai shiga Aljanna ikhlasinsa shi ne (ita la ilaha illallahun) ta katange shi daga abin da Allah ya haramta

                 >>>>(DARASI)<<<< 

Kalmar La ilaha illallahu kalma ce mai kunshe da ma'anar bara'a da tawaye daga wanin Allah don haka tsarkakakkiyar kalmar La ilaha illallahu ita ce wacce ma'abucinta ya nesanta ga bin umarnin wani ba Allah ba tare da katanguwa daga sa6awa umurnin Allah.
Yan Uwa da Abokan Arziki Barkan mu da wannan lokaci, dafan kowa yayi juma'a lafiya.

Kaduna press
11/9/2020.