Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

MATA AMANAR ALLAH NE.


Az-zahra Badamasi Ishaq
Kaduna Press
16/9/2020.

Da sunan Allah buwayi mafi girma da daukaka.., Allah ina rogonka daka ninka salati ga mafi soyuwarka Annibi muhammad da Allulbytinsa ma'abota tsarki..

Lallai bisa nazari da la'akari da wasu al'amura da suke kasance wa acikin wannan al'umma tamu naga yadace nayi ammani da dan karamin sanina da tinanina  nadanyi dan tsokaci akan wannan mas'ala..

Acikin wani Hadisi Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: mata amanar Allah ne kada ku cutar dasu kuma kada ku kuntata musu."

idan hakace mace har kullum bata wuce daya daga cikin wadan nan imma dai ta kasance uwa, "ya, mata, kanwa koh yaya.

Harkullum anata fadin mace tazama tagari tazama tagari saidai haryau banji anfada yanda za'a taimaka musu wajen zama nagarin ba.

Idan mukayi la'akari zamuga ita mace har abada tana under control ne bi ma'ana sai yanda akayi da ita, dalilina na cewa hakan kuwa zaizo anan gaba.


*Shinwai wacece ma mace..?*
mace ita jensice na biyu daga halittar dan Adam, ma'ana itace kishiyar halittar namiji Allah (T) ya dora mace bisa conditions na haihuwa, haila da wasu mabanbantan yanayin halitta tsakaninta da namiji.
Darajar da mace take dashi a wurin Allah (T) batada bambanci da darajar namiji. hakika mace tana rukunin farko na halittar da sukafi daraja a wurin Allah wato yan Adam.
Ayoyin Qurani sun bayyana falala daraja, kyakkyawan sakamako na masu imanine bisa daidaitawa tsakanin maza da mata, batare da rabewa tsakanin mace da namiji na idan har kasamu wata aya data ambaci sigar maza to hakika bazata kammala ba saita ambato sigar mata.

acikin suratul- tauba  aya ta 9-17 Allah (T)  yana cewa: ```Muminai maza da muminai mata kuwa masoya juna ne, suna umarni da aikata alheri kuma suna hani da daga mummunan aiki.```

don ganin wasu misalai duba suratul Ahzab aya ta 30, da suratul Hadid aya ta 55-12, suratul 49 ayata 13.

Acikin halittun Allah mace ta kasance tamkar sarauniya, domin ita rayuwar ta tin daga haihuwarta har zuwa tsufanta ana rainunta ne namiji shine yake da ikon kulawa da ita, misali ciyar da ita, ya tufatar da ita, da kuma tarbiyyah da lafiyarta.

kamar yanda bincike ya nuna mace bata da banbanci da namiji wajan matsayi a wurin Allah (T) saidai ubangiji bisa hikimar sa ya sanya banbanci tsakanin halayyah tsakanin mace da namiji.
Allah (T) cikin hikimarsa ya azurta mace halaye kamar haka; Hukuri, Tausayi, Sanyin jiki Saukin Dabi'a da Sanyin Murya.

zanyi bayani akan masu muhimmanci a wannan maudu'in.

Hakuri, Allah ya azurta mace da baiwar hakuri fiye da namiji, yayinda ta tsinci kanta cikin wata jarabawa takan iya jurewa fiyeda tinani kuma saboda hakurinta takan iya jure rainon yara da duk matsalolin su.

Tausayi, Allah (T) ya halicci mace da baiwar hakuri, hakan ya kara bayyanar da rauninta acikin al'ummah. 

Saukin dabi'a, ko nace sauqin hali, mace ta kasance tanada saukin hali babu wuya a juyata asarrafata yadda akeso kuma acanja mata ra'ayi akan wani abu data tsayu akanshi.

Abin lura anan tinda har dabi'ar mace ta kasance me sauqi ce za a iya canjata akowanne lukaci toh kunga ashe akwai bukatar duk wanda zai shigo rayuwarta yaji tsoron Allah akan al'amarinta idan har kabada gudummawa wurin lalacewar yar wasu shin kataba tinani akan taka "yar kuwa 
domin tamkar ka siyarwa iyalinka tikitin bala'i ne.

Allah (T) ya sanya mace itace abokiyar rayuwar namiji ya umurci maza dasu kasance masu kyautawa agaresu.

wasallallahu ala muhammad wa ali muhammad..

Post a Comment

0 Comments

Close Menu