MUZAHARAR LABBAIKA RASULULLAH A KADUNA...!!!

-KADUNA PRESS.

A yau juma'a 18/09/2020 'yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzakiy (H) na Da'irar Kaduna da kewaye suka fito domin bin sahun takwarorinsu na sauran Da'irori domin nunawa duniya cewa suna tare da Manzon Allah (S), abisa zagin da gidan jaridar Charlie hebdo mai daurin gindin gwamnatin faransa tayi masa.

Sannan da kara jaddadawa gwamnatin tarayyar Nigeria cewa lallai ta gaggauta sakin Jagora Sheikh Zakzakiy ba bisa ka'ida ba, kamar yadda babbar kotun mai shari'a Mr. Kolawale mai lamba ta shida dake da mazauni a Abuja ta hukumta kana tace a biyashi diyya tare da matarsa na tsare su da akayi ba bisa ka'ida ba, sannan da kuma bata musu lokaci da akayi.

Muzaharar da Sheikh Aliyu Tirmidhiy wakilin 'yan uwa na Da'irar Kaduna ya jagoranta, andai farata ne misalin karfe daya na rana, kuma an farotane daga kano road by Ahmadu bello way, aka rufeta a co-oparetive duk akan ahmadu bello way tsakiyar garin Kaduna.

Mahalartan dai suna rike ne da kwalayen dake dauke da rubutu "bamu yarda da zagin Annabi ba, da kuma hotunan Sheikh Zakzakiy da aka rubuta #FREE SHEIKH ZAKZAKIY. Sannan suna tafe suna janye da tutar faransa akasa, kana suna tafe suna rera baitocin rashin amincewa da cin zarafin Ma'aiki (S), da kuma na neman ganin an saki Jagora Sheikh Zakzakiy.

Bayan anzo inda za'a rufe muzaharar ne aka kona tutar kasar faransa akayi addu'a aka sallami kowa.

Andai fara kuma an kammala muzaharar lami lafiya ba tare da tasarwa da wani hankalin ba.

-KNPRSCD 06.

-18/09/2020.