Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

TAKARDAR SANARWAR MANEMA LABARAI

Kisan da 'yan Sanda suka yi a Kaduna: Ya zama wajibi a taka wa Gwamna Elrufa'i burki

Gangamin jami'an tsaro 'yan Sanda dauke da muggan makamai a yau (30/08/2020) sun bude wuta a garin Zariya da kuma cikin garin Kaduna a kan 'yan uwa Musulmi masu juyayi jim kadan bayan kammala Muzaharar Ashura ta wannan shekara (Taron addini wanda al'ummar Musulmi Mabiya Mazhabar Shi'a suke gudanarwa a dukkanin fadin duniya a irin wannan rana ta goma ga watan Almuharram). A sanadiyyar wannan mummunan hari na ta'addanci, dan’uwa Musulmi almajirin Shaikh Zakzaky da wani mutum daban sun rasa ransu a garin Kaduna nan take, a yayin da kuma da dama suka jikkata a cikin garin na Kaduna da kuma Zariya. Daga bisani kuma a ranar Talata wani dan’uwa musulmi ya rasa ransa sanadiyyar harbin sa a kirji da ‘yan sandan suka yi.

Babu tantama, wadannan jami'an tsaro 'yan Sanda suna karbar umarni ne daga Gwamnan jihar Kaduna, wanda dama shi ke da alhakin irin wannan harin da aka kaddamar a cikin garin na Kaduna sati guda da ya gabata, lamarin da shi ma ya sabbaba rasa rayukan mutane uku da kuma barnata gidaje da ababen hawa, wanda wadannan mabarnatan jami'an tsaro 'yan Sanda suka aikata.

Ya kamata a lura da cewa, an gudanar da irin wannan Muzahara ta Ashura a yau a cikin manyan birane da garuruwa da ke fadin tarayyar Nijeriya, ciki kuwa har da wadansu jihohin Kudancin Nijeriya ba tare da an samu wata matsala ko hatsaniya ba, in ban da Zariya da Kaduna, inda aka kaddamar da hari na ta'addanci a kan masu Muzaharar lumana ta Ashura. Haka nan kuma wadannan jami'an tsaro 'yan ina-da-kisa na Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru Elrufa'i sun kama mutane da dama.

Harkar Musulunci a Nijeriya tana kira ga daukacin 'yan Nijeriya ma'abota hankali da adalci da ma al'ummatan duniya da su taka wa Gwamna Elrufa'i na Jihar Kaduna burki, su hana shi ci gaba da shekar da jinainan fararen hula 'yan Shi'a wadanda ba su dauke da makami, kuma ba su aikata laifin komai ba.

Abin da ke biye hotuna ne na 'yan Shi'a wadanda harin ta'addancin jami'an tsaro ya rutsa da su a yau.

SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA. 
30/08/2020
Fassarar Zaharaddeen Sani Malumfashi.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu