Kaduna press✍🏼

© 13/9/2020

Da sunan Allah Mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad (s.a.w) da Iyalan gidan sa tsarkaka, da kuma sahabban sa managarta. 

A wadan nan kwanakin na dauki wannan fagen ne na abun da ya shafi aikin jarida, kasantuwar yadda naga wasu ba'adin mutane na ta aiki na rashin kan gado, da kawo husuma da rarraba tsakanin al'umma da sunan aikin media ko abin da ya yi kama da haka. Magana ta gaskiya aikin jarida aiki ne na masu ilimi da kwazo da sanin ya kamata, kana kuma aiki ne mai tsari, ba kamar yadda jamar mu ke kallon sa ba, kowa ya samu babban waya ya zama mai bada labari da sharhi a kafafen sada zumunta. Akwai rabe rabe da tsari masu yawa a aikin jarida..

A aikin jarida akwai mai rubutu da nazarin labarai. Akwai mai rahoto na nesa, wanda ke dauko rahoto a rediyo ko talabijin ko wani shafi (website) daga wani gari mai nisa koma daga wata kasar ta waje. Akwai kuma Dan jarida mai duba gyare gyare da yadda labari yake. Akwai kuma wanda shi aikinsa duba kuskuren rubutu. Akwai kuma wanda ke gabatar da labarai. Akwai mai daukar hoto ko video, audio.

Abun Lura A yayin Aiki Rashin Nuna Bambanci Ga Mai Bada Rahoto. 

Wanda kake bai wa labari za su yi tsammanin za ka fada masu gaskiya ne iya saninka ba tare da boye-boye ba.
Za ka kawo masu dukkan bangarorin abin da kake ba da labari a kai ba tare da nuna bambanci ga wani ba don ba ka son shi.

A takaice, tamkar ka kulla amana ne tsakaninka da masu sauraro ko masu karatu cewa ba za ka yi algushu ba wajen ba su labari.

Don haka, za su sanya ran jin gaskiyar abin da ka binciko, ko kafar ka ta watsa labarai ta biciko, ba wai shaci-fadi ba.
Babu kara gishiri, babu shafalabari shuni.

Hakan kuwa ba zai yiwu ba sai ka ajiye soyayyar ka a gefe guda, kiyayyar ka a gefe guda a lokacin da ka zo watsa ma jama’a abin da kake dauke da shi.
 
Dole ka kiya ye kalmomin muzantawa.

Misali, idan ka ce dubun wani wanda ake zargi ta cika, tamkar ka zartar da hukuncin cewa: ya dade tabka laifuka ke nan, yanzu kuma Allah ya kama shi.
Kai dai tsaya a kan an kama wani da ake zargi. Amma in kotu ce ta same shi da laifi, don ka ce yana da laifin ba ka yi laifi ba.

An cabke...” ta yi kama da abin da kake murnar aukuwarsa, yayin da “An kama...” ba ta da alama nuna ra’ayi.

An tasa keyarsa...” ta yi kama da wulakanci, yayin da “An kai shi...” ba ta nuni da wulakanci.

A BUNDA ZA A GUDA A YAYIN  A RAHOTO

A rahoto ko hira kuma, guji bai wa wani bangare muhimmanci fiye da wani, ko bai wa wani damar fadin ta bakinsa fiye da wani, ko kuma kalubalantar wani fiye da wani a hirarka.

Lallai a ji babu fifita wani a kan wani a duk wani abu da ka watsa, wannan shi ne abun da muka rasa a yayin da yan jarida ke rahoto a kan Allama Sheikh Zakzaky da almajiran sa.

Insha Allah zamu cigaba da ga inda muka tsaya.

Ku cigaba dai da kasancewa da kd press

              ________S.Y_________