Kaduna press✍🏼
12/9/2020

Da sunan Allah Mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad (s.a.w) da Iyalan gidan sa tsarkaka.

A yau na dauki alkalami zan yi rubutu ga me da aikin jarida ( journalist), sabo da yadda na ga kowa da ya bushi iska sai ya fara kiran kansa dan jarida, musamman ma wadanda ke yawaita rubutu a shafukan sada zumunta. 
A tsawon tarihi banta bagani ko jin wanda ya tsinci allura ba sai ya zama likita, ko wanda ya tsinci key mota sai ya zama direba, amma kasantuwar Allah ya kawo mu zamani manyan waya sun yawaita a hannun mutatane, haka sai ya ba al'umma damar tofa albarkacin bakin su a kafafen sada zumunta, da kuma saduwa da sauran jama'a na sauran kasashe, da zaran mutun ya mallaki baban waya (Android) shike nan sai ya fara rubutu da ba da rahoto a kafafen sada zumunta (social media), da su nan dan Media, ko kaga mutum ya bude blog ya na ta copy and paste, yana bi shafufukan jama'a da kafafen yada labarai yana kwafo labarai, da kuma daukan rubuce rubece a kafafen sada zumunta (social media). Bai da manufa bai da hadafi, in ma yana da shi bai wuce na neman suna ba. Bai san illar da ke tartare da abun da yake yi ba.
Magana ta gaskiya aikin jarida ba aiki ne da kawai mutum zai wayi gari ya ji ya iya ba. Ko da ya iya rubuta da iya surutu ba su ne su ke nuni da mutum ya iya aikin jarida ba. Domin aikin jarida ba rubuta kagaggen labari bane, balle a ce in ka iya ko ka iya kago labarai shikenan ka zama dan jarida. 

Kamar yadda ake karantar kowane aiki haka ake karantar aikin jarida, yana da ka'idojin rubutu. 

Ko da yake mafi yawancin jama'a ma ba su fahimci wanene dan jarida ba. Domin kuwa na kan ga ko da rubutu mutum ya ke yi ana wallafawa a jaridu sai inji jama'a suna kiransa da dan jarida. 

Haka ma idan mutum yana gabatar da shiri a gidan rediyo ko talabijin, ba tare da la'akari da wane irin shiri yake gabatarwa ba, sai kaji mutane suna kiransa da dan jarida. Kafin muyi nisa ya kamata mu fara sanin waye dan jarida?

WANE NE DAN JARIDA?

Dan jarida shine wanda ya yi karatu tun daga firamare zuwa sakandire sannan ya karanci aikin, yake samo labarai yana yadawa a gidajen talabijin da jaridu. Ana samun Dan jarida mai zaman kansa ko kuma wanda zai rinka yima wata kafar yada labarai, Rediyo ko Talabijin Aiki, Akwai ire iren Yan jaridu kamar, Mai rahoto (wanda yake bincike kuma ya rubuta sannan ya kawo rahoto.) Yan jaridu suna rubuta labarai da sharhi a kafafen yada labaru. Suna yin bincike ne da hira da mutane da tambayoyi wajen rubuta labaru da rahotannin su. 
A takaice dai wannan shine dan jarida. 

Na san wani zai yi min tambaya kamar haka: Shin 'yan jaridar da su ke aiki a Gidajen Rediyo da Talabijin ba yan jarida bane? 
Amsa: Suma 'yan jarida ne, masana kuma tsofaffin yan jarida sun ce: akwai ban-banci tsakanin dan jarida da ma'aikacin gidan Rediyo da Talabijin. Inda suka ce dan jarida shine wanda yake aiki a Gidan Jarida, shi kuma wanda ya ke aiki a Gidan Rediyo sunansa ma'aikacin Gidan Rediyo, haka wanda yake aiki a Talabijin sunansa ma'aikacin Gidan Talabijin.

Amma idan mukayi la'akari da wadansu abubuwa ma iya cewa akwai ma'aikatan Gidan Rediyon da a iya kiransu 'yan jarida, domin kuwa aikin da suke yi aiki ne da babu wanda zai iya yinsa sai dan jarida. 
Yana dakyau mu sani aikin Rediyo aiki ne da ya kasu kashi-kashi, wanda haka ne ma yasa kusan kowane Gidan Rediyo suke kasa ma'akatansu sassa daban-daban. 
Misali: Sashin labarai, sashin shirye-shirye, sashin tallace-tallace, da sauransu. 

Idan muka dauki sashin labarai za mu ga cewa kusan duk ayyukan da ake yi a sashin ba kowa ne zai iya ba sai dan jarida, domin ba zai yiwu a dauki wanda bai iya aikin jarida ba ace shi zai tace labarai, ko ace shi zai tsara labarai, ko kuma shi zai tattara labarai. Kunga kenan a na iya cewa a cikin ma'aitan Rediyo akwai 'yan jarida. 

Idan muka waiwaya wani sashin kuma za mu ga akwai ayyukan da ba lallai ne sai mutum ya karanci aikin jarida zai yi su ba. Misali: Idan muka kalli sashin shirye-shirye za mu ga cewa akwai shirye-shiryen da ba lallai ne sai wanda ya karanci aikin jarida zai iya gabatar da su ba. Akwai shirin da za a iya baiwa mutum ya rika gabatarwa saboda yana da kwarewa akan abin da shirin ya ke tabowa. Misali: Shirin kwallon kafa, Shirin barkwanci, da sauransu.

A na iya nemo wanda ya ke da sani akan harkar kwallon kafa ya rika gabatar shiri akan kwallon kafa. Haka shirin barkwanci, shima a na iya nemo wani ma'aboci sa ko ma'abotan barkwanci su rika gabatarwa. Dadai sauransu.

Shima sashin tallace-tallace ba lallai sai dan jarida ne zai iya aiki a sashin ba.

Idan an fahimci bayanan da mu ka yi a sama, za mu ga ashe ba kowane ma'aikacin gidan Rediyo da Talabijin ne dan jarida ba. Haka kuma za mu ga maganar masana kuma tsofaffin yan jarida ta fito, wato akwai dan jarida akwai kuma ma'aikacin gidan rediyo da Talabijin. 

Insha Allah rubutu na gaba za mu dora daga inda muka tsaya.

Kawai ku kasance tare da Kaduna press.

Kaduna press
12/9/2020