Kaduna press✍🏻
    ©14/09/2020

– Daga cikin jawabin Shaikh Shahid Mukhtar Sahabi Kaduna.

“Lokacin Malam na gidan yari mu muna waje (kafin waki'ar Abacha), sai muka kaiwa su Malam korafin cewa ana cikin yanayi. To daga cikin nasihar da Malam yayi mana sai ya karanto mana wata aya a cikin Al'Qur'ani mai tsarki, inda Allah Yake cewa: “...In takunuuw ta'alamuuna fa innahum ya'alamuwna kama ta'alamuwn, wa tarjuna minallahi malaa yarjuwn, wa kanallahu aliman hakimaa”.

“Ma'ana, idan kun kasance kuna jin radadi (dangane da takurawar azzalumai da sukeyi muku akan hanyar Allah) to suma sunajin wannan radadin da kuke ji, sannan ku Muminai kuna kaunar wani rabo daga Allah, wanda su kuma azzalumai basu da wananan rabon. 

“A lokacin da Malam Ya karanto mana wannan ayar sai naji kamar bamu taba karanta wannan ayar ba, kamar wahayi akayi masa a lokacin (sabida yadda ayar ta dace da halin da muke ciki). To wannan albarkacin Jagora kenan. Shi Qur'anin da kake karantawa, duk lokacin da Jagoran ya karanta maka sai kaji kamar a lokacin aka saukar da ayar. Sabida ba zaka gane ma'anarta ba koda kuwa kayi ‘PhD’ a Luggatul Arabiyya, to Shehinka na addini wani larabcin sai ya karantar dakai.”

– Lawal Muhammad
@ Kaduna press✍🏻
    ©14/09/2020