KIRAN A SAKI SHEIKH ZAKZAKIY A KADUNA-KADUNA PRESS.

Yau alhamis 22/10/2020 'yan uwa musulmi almajiran Jagora Sheikh Zakzakiy (H) mazauna Da'irar Kaduna da kewaye sun sake fitowa a cigaba da daukar matakan da suka dace wanda basu sabawa shari'a ba don ganin cewa an sakko Jagora Sheikh Zakzakiy ba bisa ka'ida ba.'Yan uwan sun gudanar da muzahara ne da misalin karfe shida 06:00pm, na yammacin wannan rana.

Muzaharar wadda ta samu halartar daruruwan almajiran na Sheikh Zakzakiy dai anfarata ne daga kofar poly dake daura da asibitin Yusuf Dan Tsoho (Asibitin Dutse) T/wada, sannan aka biyo ta titin Sokoto Road da ya nufi K/bacci, andai rufe muzaharar ne a dai-dai Randa bawul na K/bacci.Andai fara muzaharar lafiya, kuma ankammala ta lami-lafiya ba tare da tayarwa da kowa hankali ba.

-KNPRCD 06.

-22/10/2020.