Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Shekarau Biyar Da Kisan Kiyashin Zaria

SHEKARU BIYAR DA WAQI'AR ZARIA...-Kaduna Press

A yau litinin 19/10/2020, 01/03/1443 'yan uwa almajiran Sheikh Zakzakiy na Da'irar Kaduna da kewaye suka fito domin subi sahun sauran 'yan uwansu na da'irori na yin muzaharar tunawa da shekaru biyar da waqi'ar Zaria.'Yan uwan sun fito mazansu da matansu manya da yaransu, akan babban titin tsakiyar jihar Kaduna Ahmadu Bello Way.

Masu muzaharar suna tafe suna rera waqene mai bayyana irin ta'addanci da ta'annutin da sojojin Nigeria suka aiwatar a dai-dai irin wannan rana a karshen shekarar 2015.

Sheikh Aliyu Tirmidhiy ne ya jagoranci Muzaharar, wadda aka fara da misalin karfe biyu dai-dai na rana.

Andai fara Muzaharar ne kuma an kammala lami-lafiya, ba tare da tasarwa da kowa hankali ba.

-KNPRCD 06.

-19/10/2020.

01/03/1443.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu