Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

YADDA A KA GUDANAR DA SAKA TUTAR MUHAMMAD RASULLAH A DA'IRAR KADUNA...


A jiya litinin 19 ga watan 10 shekara 2020 yan uwa almajiran sheikh Zakzaky na da'irar Kaduna sun gudanar da saka tutar Muhammad Rasullah, an gabatar da fareti da karate da wakoki, domin girmama wa ga Manzon tsira (S), sannan a ka saka tutar. 
Sannan a ka mika abun magana a ga wakilin yan uwa na garin Kaduna Malam Aliyu Tirmizi ya gabatar da jawabi ga mahalarta taron da kuma Isar da sako ga sauran al'umma game dalilin canza tuta daga baka zuwa fara, inda yace: kamar yadda a ka saba kowace ranar daya ga Rabi'ul Auwal ta kowace shekara ana saka wannan tutar ne a Husainiyya zaria, kafin harin sojoji najeriya a shekara 2015, hakan ya sanya harkan ya kara fadi, yazama kowace gari ana bikin sanya wannan tutar, in da ya kara da cewa: an canza tutar ne daga baki zuwa fari sakamakon kwanakin juyayi sun wuce da kuma shigowar kwanakin bukukuwan tunawa da rahamar Ubangiji gare mu, na haihuwar mai Albarka Manzon Allah (S).

Ya kuma yi kira ga al'umma da su kara zage damtse don nuna kishin su ga Manzo (S), inda ya kara Allah wadai ga wadan da suka ci zarafin Manzon Allah a Faransa, ya kuma kira ga al'umma da su fito yin Allah wadai, i dan irin hakan ya sake faruwa.
A kar she ya tunatar da al'umma game da harin ta'addancin sojojin Najeriya a ranar daya ga Rabi'ul Auwal wanda yayi dai-dai da ranar 12 ga watan 12 shekar 2015, Inda Tukur burtai kar kashin gwamnatin Buhari ya jagoranci kisan Almajiran sheikh Zakzaky sama da dubu (1000+), da kona muhalai na harkar musulunci, da nufin kashe jagoran Harkar Musulunci Sheikh Zakzaky. In da suka kashe masa yaya uku, da kona yayarsa da ranta, duk a gabansa. Sannan suka harbe shi da iyalin shi, tsawon shekara biyar (5) suna cigaba da tsare shi batare da wani dalili ba.
An gudanar da wannan taro lafiya an tashi lafiya.

Kd-001/007
Kaduna Press.
20/10/2020

Post a Comment

0 Comments

Close Menu