Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

YANAYIN LARABAWA KAFIN AIKO ANNABILarabawa a wancan lokacin -na jahiliyya- ba su kasance ma'abuta littafi ko mabiya wani saukakken addini ba, balle har -littafin ko addinin- ya daga matsayinsu na tunani, zamantakewa da wayewa. Jahilci da duhun kai da karkacewa ne kawai suka mamaye tsibirin larabawa, kuma suke wasa da hankula da akida.

Larabawa sun kasance suna bautar gumaka, aljanu, taurari da Mala'iku; kadan daga cikin su ne suka kasance a kan addinan Annabi Ibrahim, Musa da Isa (a.s).

A irin wannan halin al'ummun da suka fi labarawa wayewa da ci-gaba, wato Yahudawa, Nasarawa da Majusawa, suka kasance. Su ma sun kasance karkashin kamun rayuwar jahiliyya, bata da karkacewar akida da zaluncin siyasa. Suna karkashin masu dagawa.

Akwai wasu manyan dauloli uku da ke kewaye da larabawa. Akwai daular Rum daga yamma, daular Farisa daga gabas, sai daular Habashawa daga kudu. Wadannan su ke da karfin siyasa da wayewa a wancan lokacin.

Kasancewar larabawan da ke garin Makka da kewaye ba su san ma'anar hukuma ba, sun kasance suna raye karkashin mulkin kabilanci da shugabancin wasu manya masu karfi a kan talakawa da bayi.

A irin wannan duhun zamantakewa, mace ta kasance tana dandana rayuwar wahala da rashin mutunci. Ba ta da hakki, ba daraja; saboda ita, a al'adar wannan al'umma ta jahiliyya, mallakar namiji ce, ana gadon ta kamar yadda ake gadon dabbobi da abubuwan mallaka. 'Ya'ya sun kasance suna gadon matan ubanninsu kuma su aure su.

Dayan su ya kasance idan aka haifar masa 'ya mace sai bakin ciki ya rufe shi, ya shiga tsoron kunyata da bacin suna, sai ya dauki matakin kashe ta ko bisne ta da rai ko ya karbeta cikin wulakanci da kiyayya.

Yayin da muka fahimci wannan hakika, za mu iya fahimtar Musulunci da girman Annabinsa (s.a.w.a); wanda, bisa yardar Allah, ya iya ceto dan Adam da sanya shi a kan hanyar madaukakiyar wayewa da daidaituwar dabi'a da shiriya.

Hakika Allah Madaukaki Ya siffanta sakon AnnabinSa da fadarsa cewa:

Hakika haske ya zo muku daga Allah da littafi mabayyani. Da shi, Allah na shiryar da wanda ya bi yardarsa tafarkin tsira, kuma yana fitar da su daga duhu zuwa haske da izinin Shi, kuma Yana shiryar da hanya madaidaiciya. (Ma'ida: 15-16)

Post a Comment

0 Comments

Close Menu