DA'IRAR KADUNA TA GUDANAR DA ZAMAN WAFATIN MANZO (S).-KADUNA PRESS.

A jiya juma'a 28/safar/1441-16/10/2020. 'Yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzakiy (H) na da'irar Kaduna sun shirya kuma sun gabatar da zaman juyayin tunawa da wafatin Manzon Tsira (S) a wasu bangarorin halkoki daga cikin halkokin dake cikin garin na Kaduna.'Yan uwan sun shirya tarurrukan ne a halkar Rasulul'akram (S), halkar Ameerul Muminin (K) da kuma halkar Imam Mahadiy (A), da wadansu halkoki a cikin Da'irar.'Yan uwan sun gayyato Malamai daban-daban daga wurare mabanbanta domin gabatar musu da jawabai a muhallin tarurrukan.Malaman dai sun gabatar da jawabai ne tiryan-tiryan, filla-filla akan waqi'ar data faru a ranar da Manzon Allah yayi wafati, kama daga abubuwan da suka fara faruwa tun daga hajjin da Manzo (S) yayi ta bankwana, har zuwa bayan wafatinsa, da abubuwan da akaiwa Sayyida Zahra da Imam Ali (A).Bayan kammala jawaban ne aka buga kirji akayi wakokin juyayi aka koka sosai, sannan akayi addu'a aka sallami kowa.

-KNPRCD 06.

-16/10/2020.

-28/SAF/1441.