Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

ABUBUWAN DA SUKA FARU DA ANNABI DA MUSULUNCI A MAKKA.


Yan uwa masu karatu barkan mu da sake saduwa da Ku, a filin mu na tinatarwa, Rubutun mu na yau zai yi magana a kan: Hijirar Farko Zuwa Habasha, Tafiya Zuwa Da'ifa, Sanya Takunkumi ga Musulmi, Ganawa da Wakilan Mutanen Madina, Shekarar Bakin Ciki, Mubaya'a ta Farko a Akaba.

HIJIRA ZUWA HABASHA

Bayan da Manzon Allah (s) ya fito fili da wannan kira nasa da kuma irin karbar da al'umma suka yi wa kiran, sai kafiran Makka suka fara tunanin hanyoyin da za su bi wajen kawo karshen wannan barazana da take fuskantarsu. Don haka sai suka fito wa lamarin ta hanyoyi daban-daban, daga cikin hanyoyin kuwa har takurawa al'ummar musulmin da kuma azabtar da su. sai Manzo (s.a.w.a) ya ga cewa bari ya yi wa wani adadi daga mabiyansa izini da yin hijira zuwa Habasha, don ya samar musu kariya da matsera daga takurawa.

Don haka sai mazaje goma sha daya da mata hudu suka yi hijirar, suka saura a Habasha har na tsawon watanni uku, har zuwa lokacin da labari ya isa gare su cewa Kuraishawa sun mika kai. Wannan ya sa suka dawo Makka, sai dai sun sami cewa Kuraishawa na nan da halinsu ba su canza ba, wato dai suna ci gaba da cutar da Musulmi da azabtar da su.

Sai Manzo (s.a.w.a) ya hore su da sake yin hijira zuwa Habasha. A wannan karon adadinsu ya kai maza tamanin mata goma karkashin ja-gorancin Ja'afar dan Abi Dalib.

Kuraishawa dai sun yi matukar tsorata da wannan hijira, don haka sai suka yi kokarin dawo da su, in ban da cewa sarkin Habasha Najjashi, wanda ke bin addinin Annabi Isa (a.s) a wannan lokacin, ya ki yarda da bukatun 'yan aiken Kuraishawa, wato Amr bin As da Ammara bin Walid. 'Yan aiken na Kuraishawa sun yi kokarin shafa wa musulmin bakin fenti a wajen sarkin Habasha don ya ki karbar masu hijirar; bugu da kari kuma suna dauke da kyautuka masu yawa daga Kuraishawan zuwa gare shi; sai dai kuma jawabin da Ja'afar dan Abi Dalib ya yi a gaban sarkin ya bata musu shiri da kuma sanya sarkin ya ki amincewa da bukatan 'yan aiken, inda ya ke cewa:

Ya kai wannan sarki, hakika mun kasance mutanen jahiliyya Muna bautar gumaka, muna cin mushe, muna aikata alfasha, ba ma sadar da zumunci, muna munana makotaka, mai karfi a cikinmu na danne mai rauni. Haka muka kasance har Allah Ya aiko da Manzo zuwa gare mu, wanda mun san danganensa da gaskiyarsa, rikon amanarsa da kamun kan sa; sai ya kira mu zuwa ga Allah don mu kadaita Shi kuma mu bauta mi Shi, mu kuma janye daga abubuwan da muka kasance, mu da iyayenmu, muna bauta musu na daga duwatsu da gumaka. Ya hore mu da fadar gaskiya, rokon amana, sadar da zumunci, kyautata makotaka da kamewa daga da abubuwan da aka haramta da zubar da jinni. Ya kuma hana mu aikata alfasha, shedar zur, cin dukiyar maraya da yin kazafi. Haka ya hore mu da bautar Allah Shi kadai ba tare da mun hada Shi da komai ba. Ya hore mu da yin salla da zakka da azumi.

Sai Najjashi ya ce masa: "Ko kana a tare da kai akwai wani abu daga abin da Manzo Muhammadu ya zo da shi daga Allah?".

Sai Ja'afar ya ce na'am. Sai ya karanta masa wani sashi na Surar Maryam. Jin wannan aya, sai Najashi da wadanda suke tare da shi na daga malaman Kirista suka fashe da kuka. Sai Najashi ya ce: " Hakika da wannan da abin da Isa ya zo da shi sun fito ne daga tushe guda."

SANYA TAKUNKUMI GA MUSULMI

Lalacewan shirin Kuraishawa na kawo cikas ga hijira zuwa Habasha ya kara kaimin adawarsu da da'awar Musulunci, don haka sai suka kuduri aniyar lankayawa Bani Hashim takunkumin cinikayya, cudanya da auratayya; sai suka rubuta haka a wata takarda wadda mutane arba'in daga shugabannin Kuraishawa suka rattabawa hannu a kai. Sai suka kange Banu Hashim a Shi'ibi Abi Dalib, suka zama ba sa fita daga wannan guri sai a lokutan Ummura a watan Rajab, da lokacin aikin Haji a watan Zul-hijja saboda girman matsayin a tsakaninsu da sauran Kuraishawa.

Musulmi sun shiga wani mawuyacin hali matuka, saboda hatta abincin da zai ishe su ba su da shi, kunci ya kai musu ko'ina. Haka wannan takunkumi ya ci gaba har tsawon shekaru uku, lokacin da takunkumin ya kawo kare yayin da Allah Ya turo sari ya cinye wannan takarda da aka sanyawa hannu, bai bar kome ba sai kalmar Bismikal-Lahumma (wato da SunanKa ya Allah), dake rubuce a saman ta. Wannan al'amari ya yi matukar ruda mushrikai, ya kuma sa musu karin dalili a kan gaskiyar da'awar Manzo (s.a.w.a).

SHEKARAR BAKIN CIKI

Duk da cewa takunkumi ya kare, sai dai haka bai zama karshen matsaloli ba; domin Khadija bint Khuwailid, matar Annabi (s.a.w.a) kuma babbar uwar muminai, wadda ta kasance farkon wadda ta bada gaskiya da shi ta kuma gaskata shi, ta kuma yi tarayya da shi cikin wahalhalun isar da sako; ta bayar da dukiyarta saboda Allah. Rasuwarta ta kasance kafin hijira (zuwa Madina) da shekaru uku, kuma a watan Ramalana mai alfarma. Manzo (s.a.w.a) ya ji wannan mutuwa kuma ya yi bakin ciki matuka.

Bayan wafatin Khadija (RA) da kwanaki uku kuma sai Abu Dalib, mai kariya ga Annabi kuma madogaran sakonsa, shi ma ya rasu. Labarin rasuwar wannan baffa na shi ya sa shi cikin karin bakin ciki, yayin da ya je wajen gawarsa, ya shafi gefen goshinsa na dama da na hagu, sannan ya ce:

Ya baffa, ka reni yaro, ka rike maraya kuma ka yi taimako mai girma, Allah Ya saka maka da alheri a kan abin da ka yi min.

Saboda tsananin tasirin wadannan abubuwa biyu a ci-gaban yunkurin tarihin Musulunci ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya sa wa wannan shekara suna Shekarar Bakin Ciki.
   

TAFIYA ZUWA DA'IFA

Saboda kunci da damuwar rashin Matarsa da Baffansa, kana kuma ga sabuwar gaba da kafiran Makka suka dasa saboda karfin gwuiwan da suka samu saboda rasuwar Abu Talib, Manzon Allah (s) ya kuduri aniyar zuwa garin Da'ifa don isar da sakon Musulunci; amma abin takaici mutanen Da'ifan ba su karbi wannan sako ba. Babu wanda ya amsa wannan kira na Manzon Allah (s) in ban da wani tsohon mabiyin addinin Kirista manomi wanda ake kira da Adhasu, shi ne kawai ya karbi Musulunci.

Larabawan Da'ifa, maimakon karbar sakon Musulunci, sai suka umarci 'yan iskan gari da kananan yara da su jefi Manzon Allah (s) da duwatsu duk inda ya tafi. Ko da Manzon Allah (s) ya ga wannan sako nasa ba zai yi wani tasiri ga wadannan mutane na Da'ifa masu kekasassun zukata ba, sai ya koma garin haihuwarsa wato Makka.
    
GANAWA DA WAKILAN MUTANEN MADINA

Bayan dawowa ma dai Manzon Allah (s) ya ci gaba da kiran mutane da kuma kabilu daban-daban zuwa ga Musulunci, sai dai kuma a wannan karon ma dai ba a samu wasu adadi mai yawa da suka karbi wannan da'awa ba.

A shekara ta goma sha daya bayan aiko Annabi ne, a lokacin da ya rika bijiro da kiransa a lokutan aikin haji ne ya hadu da wasu mutane daga Khazraj, wadda daya ce daga manyan kabilun nan biyu na Yathrib (wanda ya zama Madina bayan hijira); wadannan mutane ne kuwa suna karkashin jagorancin As'ad bn Zurar, inda ya bijiro musu da Musulunci su kuma suka amsa masa. Wannan tawaga ta yi matukar farin ciki da wannan kira da kuma imanin da suka yi da shi. Daga nan sai wannan shugaba na su ya bukaci Manzon Allah (s) da ya hada su da wani daga cikin sahabbansa don su tafi Yathrib din don ci gaba da isar da sakon Musulunci da kuma karantar da wadanda suka amshi kiran. Hakan kuwa aka yi, sai suka koma Yathrib suna kiran mutane zuwa ga Musulunci.

Komawarsu ke da wuya sai suka fara wannan da'awa da kuma kiran jama'a zuwa ga wannan sabon addini kana kuma hanyar tsira duniya da lahira da dukkanin al'umman duniya, amma fa ga wanda ya yi imani da shi. Lalle cikin dan lokaci kadan an samu nasarori kala-kala inda aka samu mutane masu yawan gaske da suka Musulunta.
    
MUBAYA'AR FARKO A AKABA

Bayan haka, a shekarar da biyo baya, sai wasu mutum goma sha biyu daga mutanen Yathrib suka je wajen Manzo (s.a.w.a) a Akabah, suka yi mishi mubaya'a a kan cewa: "ba za su hada komai da Allah ba, ba za su yi zina ba, ba za su kashe 'ya'yansu ba, ba za su yi zaluncin da suka kirkira da hannunsu da kafafuwansu ba, kuma ba za su saba masa a kan wani abu mai kyau ba; in har sun cika alkawarin to suna da Aljanna; in kuwa suka tauye wani abu daga wannan, to al'amarinsu na wajen Allah, in ya so ya azabtar da su, in ya so ya yi musu afuwa."

A lokacin aikin hajin da ya biyo bayan wannan, wato a shekara ta goma sha uku da aiko shi, sai wata babbar tawaga daga Yathrib ta yi wani taron asiri da Manzo (s.a.w.a) a Akabah; tawagar ta kunshi maza saba'in da mata biyu.

Wannan ne ya samar da wani yanayi da da'awar Musulunci za ta tsayu a kan ta wajen isar da babban sako. Sai Manzo (s.a.w.a) ya hori muminai da yin hijira zuwa Yathrib. Sai Musulmi suka yi ta kwarara, a boye cikin duhu, zuwa gidan imani, suna masu barin dukiyoyinsu da gidajensu saboda addinin Allah Madaukaki.

Kd-001/007

©4/11/2020.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu