Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

ALMIZAN TA CIKA ALKAWARI!

Masu iya magana suna cewa, “kyan alkawari cikawa,” to jaridarku mai albarka da farin jini, ALMIZAN, ta cika alkawarin da ta yi a makon jiya cewa za ta inganta bayanan da take bugawa, biyo bayan karin kudin jaridar daga N150 zuwa N200 a jaridar wannan makon.

Da ma kowace jarida ko kafar watsa labarai babban aikinta shi ne fadakarwa, ilmantarwa da nishadantarwa. To a wannan marrar, ALMIZAN ta karfafa ilmantarwa sosai, don kuwa ta fito da wasu sabbin FILAYE a jaridar mai fitowa, kuma za ta ci gaba da su a kowane mako.
 
Sabon fili na farko shi ne Tafsirin Alkur'ani Mai Girma Sauka Na Biyu, wanda a cikin sa za mu rika kawo maku Tafsirin Alkur’ani mai girma da Jagoranmu Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky ya rika yi duk Laraba kafin azzalumai su auka masa da almajiransa a Disamban 2015. 

Wani na iya cewa Tafsiri kuma a jarida? To, wannan ba ba}on abu ba ne, domin jaridar Turanci da ake kira CRESCENT INTERNATIONAL tana da filin Tafsiri, wanda Imam Muhammad Al-Asi ke gabatarwa. Kuma Alhamdulillah, daga nan ne har Shehin Malamin ya fid da littafi na Tafsirin Alkur’ani da Turanci. 

Sabon Fili na biyu da za ku samu a ALMIZAN ta makon nan sunansa: Tarjama da Sharhin littafin Nahjul Balagha, wanda Hudubobi da Kalaman Amirulmuminin Ali (AS) ne, wanda Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yake karantarwa a duk ranar Litinin.

Dukkan wadannan Filaye biyu na ilmantarwa, babban Editanmu Ibrahim Musa ne zai rika rubutawa da kula da su, don ba su cikakkiyar kulawar da ta dace da su.

Sai Fili na uku da muka karfafa, Filin Fasahar Zamani, inda a ciki a wannan makon mun kawo bayanin yadda za ku kare wayoyinku na komai da ruwanka daga sharrin masu kutse da aka fi sani da ‘Hackers’. A wannan Fili duk wasu dabaru da za su taimaka maku kan amfani da wayoyin hannunku, za mu rika kawo su sannu a hankali daga masanan abin.

A wannan makon jaridar ALMIZAN na nan tafe da Filayen da ta shahara da su irin su ALKALAMI, HATSIN BARA, TSOKACI, DANDALIN KULA DA LAFIYA, TASKAR IYALAN GIDAN MANZO, MADUBI da sahihan labarun gida da na kasashen waje.

A karshe, jaridarku ta makon nan ba ta manta da nishadantar da ku ba, don kuwa ta zo da hikayar wani LIMAMI BARAWO! Sai ka karanta za ka ji wane irin Limami ne wannan!

*Duk wannan fa a N200. Sai dai wani kuskure da muka tafka a wannan makon shi ne, ba mu rubuta canjin farashin ba. Sai muka sa N150. A gafarce mu kan hakan. N200 ce cif-cif. Da ma mun riga mun sanar tun a makon jiya.*

Wannan sako ne daga Babban Edita IBRAHIM MUSA. Da fatan za a taya mu yadawa, wato ‘sharing’.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu