>==> Kaduna Press0011 

A yau 23/11/2020 da misalin 3:00pm na rana, daruruwa yan'uwa Almajiran Sheikh Zakzaky, sun fitowa kan titin Ahmadu bello way domin cigaba da yin kira ga gwamnatin  Buhari da ta gaggauta sakin jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakin sa, wanda da take cigaba da tsarewa tun bayan harin da sojojin Najeriya su ka kai a a garin zaria a shekar 2015, ba tare da laifin komai ba.
 
Almajiran Sheikh Zakzaky sun tafi cikin tsari tare da rera wake, da kiraye kiraye a sake shi. In da a kayi tafiya mai tsawo Sannan a ka kashe muzahran.
 
Yanzu haka dai Sheikh Zakzaky (H) yana gidan kurku a nan garin Kaduna, tare da iyalansa, duniya na ta Kira da a sakeshi, amma wannan gwamnatin tana nuna halin ko in kula.
 
Anyi Muzaharar  lafiya an tashi lafiya.

Kaduna Press0011