A yau Laraba  25/11/2020 daruruwa yan'uwa Almajiran Sheikh Zakzaky, sun fitowa domin cigaba da yin kira ga gwamnatin  Najeriya da ta sakin jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa, wanda da take cigaba da tsarewa tsawon shekaru biya ba tare da laifin komai ba. tun bayan harin Ta'addancin sojojin Najeriya karkashin gwamnatin Buhari ta yi a ranar 12/12/2015, da kisan mabiyan sa sama da dubu, ciki har da ‘ya‘yansa uku, da kona yayar sa da ranta a gaban sa, da kuma sace wasu daga cikin manyan daliban sa, da daruruwa almajiran sa.
 

Du da shekarar 2016 babban Kotun dake Abuja ta wanke shi, tace: baiyi laifin komai ba, asake shi. Gwamnatin taki tayi kunnen uwar shegu da maganar.
 
 
Har yanzu a suna tsare da shi a kaduna karkashin Nasiru El rufa'i.

Duniya na ganin yadda shari'ar ta gabata a wannan satin da ya gabata , inda mukarraban gwammanti ke ta tufka da warwara, hakan na nuni da zargin da a kewa jagoran Harkan Musulunci Sheikh Ibarahim Zakzaky bai da bai da tushe bare makama. Dan haka ne muke kara kira da babbar murya zuga Al'ummar duniya da su fahimci girman zaluncin da a kawa Malam Zakzaky da Al'majiran sa. Sannan a sau Malam Zakzaky ba tare da wani sharadi ba.

 Muna Allah wadai da Ta'addancin gwamnatin Najeriya a kan malam Zakzaky, da Al'majiran sa.

Muzaharar dai ta daga ne da misalin 2:00pm a dai dai Kaduna polytechnic a nan garin kaduna, yayin da a kayi tafiya mai tsawo, a ka mike hanya ta bi ta shataletalen kasuwar barci, ta kara mike hanya har zuwa daura da kwanar chan-changi, yayin da a ka ka she muzaharar a nan.

Allah ka fatan ta rayukan Munudai da fitowar Allama Sheikh Zakzaky, ya kuma nuna mana ranar da za a kori zalunci a wannan kasar.

Kaduna Press
25/11/2020