Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

CIGABA DA SAURARAN SHARI'AR SHEIKH ZAKZAKY RANA TA BIYU ALHAMIS....


Yau Alhamis 19/11/2020 a ka ci gaba da shari'ar Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddin Ibrahim a babbar kotun jihar Kaduna, a jiya laraba 18/11/2020, mun tsaya ne a shai da na biyu, da bangaren gwamnatin Kaduna ke kawowa.

Lauyoyin dukkan bangarorin sun halara a kotu. Alkali ya iso a ka kira shaida na uku a wannan shari'a. Sunan wannan shaida Muhammadu Abba Girei, wanda tsohon Darakta ne a hukumar tsaro ta farin kaya wato DSS. Lauyan gwamnatin Jihar Kaduna, Bayero Dari ya ne mi Girei ya fada wa kotu cikakken sunansa da in da ya yi aiki na karshe. Ya ce Sunan sa Muhammadu Abba Girei kuma aikinsa na karshe shi ne Darakta Oparation  a hedikwatar DSS da ke Abuja.

Ko ya san Shaikh Zakzaky da matarsa? Ya ce eh ya san su sosai kuma lokacin da aka kawo su hukumar tsaro a shekarar 2016. Kuma shi ne ke kula da al'amuransu, wato ciyar da su da kuma yi musu hidima. Ya ce lokacin da suke hannun su wasu masu bincike na 'yan sanda sun zo daukar bayanansu Amma suka ki yarda da hakan. Wanda kuma shi bai san dalilin da ya sa Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddin Ibrahim suka ki yarda ba.

Su wa suka mika muku Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddin? Ya ce sojoji ne suka mika su. Kana ina lokacin da 'yan sanda suka zo ne man bayanansu kai kana iya? Ya ce ina asibiti tare da su Malam Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddin. Bayero Dari ya kammala tambayiyin sa.

Femi Falana SAN ya tambayi Girei cewa: lokacin da a ka kawo su Malam da Malama a wane hali ka gansu? Shin suna cikin koshin lafiya? Girei ya ce bai sani ba, saboda shi ba likita bane. Wace rana aka kawosu? Ranar 15/12/2015 aka kawosu amma shi a ranar 16/12)2015 ne ya fara ganinsu. 

Ka tabbata ranar 16/12/2015 ka gansu? Ya ce ko ka ga jini a jikinsu lokacin? Ya ce bai gani ba. Shin ka san lokacin idon Malam a fashe ya ke? Ya ce ba zai iya tunawa ba. Sun ce maka akwai harsasai a jikinsu wanda a lokacin ba a ciresu ba? Ya ce ba zai iya tunawa ba.

Lokacin da ka gansu a asibiti an kwantar da su ne? Ya amsa da cewa ba a kwantar da su ba. Sai alkali ya ce ba za ka iya tunawa ba ko ba kwantar da su ba? Ya ce ba zai iya tunawa ba. Shi ko ka san sun kwashe watanni a asibiti a kwance. Ya ce ba zai iya tunawa ba. Ko ka san cewa yan sandan da suka zo ganin su AIG Rasheed ne? Ya ce ba zai iya tunawa ba. A takardar da ka rubuta ta shaida ka ce lokacin da AIG Rasheed ya zo daukar bayanansu lokacin suna farfadowa daga raununkan da suka samu ne shiyasa ba su iya ba shi bayanan ba, shin ka san ka fadi hakan? Ya ce ba zai iya tunawa ba. Wane lokaci ka dauka tare da su? Ya ce daga 2015 zuwa 2016 in da aka yi nasa transfer zuwa Bayelsa. Amma ba zai iya tina ko wace rana bane. Ko ka san cewa a October aka yi maka transfer zuwa Bayelsa? Ya ce bai sani ba. Ranar 2 ga Disamba kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa a sake su. Ko ka san da wannan hukuncin? Ya ce bai sani ba.
Ka ce an kawosu ranar 15/12/2015 ko ka ko akwai wata oda da kuka samu na tsaresu? Ya ce bai sani ba.  Ko ka san gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa kwamitin bincike kan abin da ya faru a Zaria? Ya ce bai sani ba. Ko ka san DSS sun hana wadanda ake kara bayyana a gaban JCI? Ya ce bai sani ba.

Ka bayyana cewa jami'an tsaro na yan sanda sun zo daukar bayanan Malam da Malama in da Malam ya shaida musu cewa ba zai ce komai ba har sai an zo da Lauyoyinsa? Ya ce bai sani ba.

Yanzu kana cewa duk wanda DSS suka kama asibiti ake ajeyeshi ko da lafiyara lau? Ya amsa da cewa eh haka suke yi. Al'adarsu ne hakan. Shin ka san cewa ni Lauyan Malam sun Sha tsareni a DSS? Ya ce bai sani ba. 

Shin ba ka taba karantawa ba cewa an tsareni a DSS? Ya ce eh bai taba ba. Alkali ya sa baki, ya ce ko a jarida ba ka taba karantawa ba? Ya ce bai taba ba kuma bai taba ji ba. Falana ya ce a shekarar 1992 an kama ni ni da Cif Gani Fahewunmi in da aka hukume mu da cin amanar kasa kuma kana cikin masu bincike? Ya ce bai sani ba.
Falana SAN ya kammala tambayarsa. Lauyan Malama ya ce ba shi da wata tambaya. Kotu ta sallami Girei
Shaida na hudu a wannan shari'a ya shigo mai suna Muktar Gambo.

Lauya Bayero ya tambaye shi Ko ka san Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddin? Ya ce ya san su saboda a Unguwa daya suke zama. Kana da wata danganta da su bayan ta zama Unguwa daya? Ya kasa amsa tambayar. Lauya Bayero ya canza tambayarsa zuwa cewa shin wane irin zama kuke yi da shi? Ya ce shekaru biyu da dawowar Shaikh Zakzaky Unguwar suka Fara samun matsala da shi. Kuma ya dawo Unguwar ne a shekarar 1998.

Ko za ka fadawa kotu irin matsalar da ku ke samu da shi? Ya ce matsalar ita ce ba sa ba yan banga hadin kai kuma ba sa barin masu kayan Sarki irin yan sanda da soji shiga Unguwar. Don haka Unguwar ta zama dabdalar masu aikata miyagun laifika.
Ko za a iya fada wa kotu cikakken sunan mabiya Shaikh Zakzaky? Ya ce sunansu Shi'a. Ko zai iya lisafta yawansu? Ya ce ba zai iya ba saboda suna da yawa. Ko kun taba kai koke wurin hukuma? Ya ce sun kai koke wajen Hakimi kuma suka tafi wurin Malam Zakzaky tare da Hakimi da suka je Malam ya shaida musu cewa bai sani ba. Amma zai dauki mataki. Amma ba a yi komai ba.

Me za ka ce wa kotun kan Malam da Malama? Ba ma son zamansu a Gyallesu. Saboda suna hana mutane shiga Gyallesu sun hana wani Navy Commander shiga gidan mahaifinsa sun hana gwamnan Kaduna Ramalan Yero shiga Gyallesu. Bayero ya kammala tambayiyin sa.

Falana SAN ya tambayeshi ko kai musulmi ne? Ya ce eh. Ko kai dan Shi'a ne? Ya ce shi ba shi'a ba ne. Ko kai Sunnah ne? Ya ce eh. Ko ya san Sunnah suna yaqar Shi'a? Ya ce bai sani ba. Shin ka ce ba ka son zamansu a Unguwar? Ya amsa da cewa eh ba ya so. Ko ya san a an rusa gidan Shaikh Zakzaky a Gyallesu? Ya ce eh ya sani. Ko ya san an yi rikicin siyasa a 2011 lokacin da Buhari ya fadi zabe?  Ya ce eh ya sani.
 
Lokacin da aka yi wannan rikici Shaikh Zakzaky ya ba kiristocin da ake son kashewa kariya a gidan sa? Ya ce bai sani ba. Ko ka san cewa Shaikh Zakzaky na raba abinci ga al'ummar Gyallesu? Ya ce bai sani ba. Ka ce kai da Hakimi kun ziyarci gidan Shaikh Zakzaky, ka san cewa Buhari ya ziyarci gidan Shaikh Zakzaky don yin kamfe? Ya ce bai sani ba. Ko ka san Malam Nasiru Elrufai ya ziyarci gidan Shaikh Zakzaky don yin kamfe? Ya ce bai sani ba. Kana cikin yan bangar Gyallesu, shin kuna kula da Unguwar awa 24? Ya ce eh. Shin kasan a shekarar 2014 an kashe 'ya yan Malam 3? Ya ce eh ya sani. Shin kana da labarin Elrufai ya ziyarci gidan don yin taaziyya? Ya ce eh Yana da labarin. Ko ka san Dambazau minista ya je gidan? Ya ce bai sani ba. Ko kana da labarin hukumar kare hakkin dan adam ta qasa ta aika wakilai don jajantawa ga Malam a 2014? Ya ce bai sani ba
Shin kasan 'ya 'yan sa da aka kashe? Ya amsa da cewa ya san su a fuska? Kana da labarin ko an hukunta wadanda suka yi kisan? Ya ce ba shi da labari? Ko qungiyarku ta nema musu haqqinsu? Ya ce Mun dai je mun yi ta'aziyya.

Shin ko kana da labarin a shekarar 2015 an sake kashe 'ya'yansa uku? Ya ce ba shi da labari. Ko ya san abin da ya faru da Shaikh Zakzaky a ranar 14/12/2015? Ya ce sojoji sun je gidan Shaikh Zakzaky. Ko ya san sojoji sun kone gidan? Ya ce bai sani ba saboda yana gida kulle.
 
Zai iya tuna cewa ya bayar da shaida a gaban JCI? Ya ce eh. Ko ya san cewa JCI ta bayyana cewa mutane 347 aka kashe a Zaria? Ya ce ya ji labarin amma bai san ko JCI ce ta fada ba. Shin ko ya san wani da aka kama ake tuhumar da wannan kisan? Ya ce bai sani ba. Shin yana farin ciki da yanzu ba 'yan Shi'a a Gyallesu. Ya ce eh Yana farin ciki saboda sun sami zaman lafiya. Falana SAN ya kammala tambayarsa. Lauyan Malama ya ce ba shi da tambaya, Kotu ta sallami dan Gyallesu.

Shamsudeen Aliyu Ahmad ne wani mazaunin Gyallesu zai ba da shaita ta 5. Ya ce shi tela ne da ke dinki a Madaki road Gyallesu. Bayero ko ka san Shaikh Zakzaky da matarsa Malama Zeenatuddin? Ya ce eh ya san su saboda shagonsa yana layi daya ne da gidansu.
 
Me za ka iya tuna ya faru da kai a wata rana ta asabar a shekarar 2013 Ya ce a shekarar 2013 wata rana yana zaune a shago sai ga yaran Malam da baro sun zo suna kwashe duwatsun da muka tare hanya saboda qura na bata mana kayan da muke dinki. Shi ne na ce ba za mu bari su kashe ba. Suka ce mun sa ne saboda malaminsu. Ina cikin magana da su sai ga mota cike da makamai zan gudu kenan sai suka sare ni a kai. Daga nan sai muka tafi wurin 'yan sanda muka kai koke. Sai aka kaini asibiti.
Falana SAN ya tambayeshi ko ya san wadanda suka sare shi? Ya amsa da cewa bai san su ba. Falana SAN ya kammala tambayarsa. Lauyan Malama ya ce bai da tambaya

Musa Isiyaku shi ne mai ba da shaida na 6.  Ya ce shi ma mazaunin Gyallesu ne ya ce yana zaune a gida mai lamba 21 Sarkin Yaki Gyallesu. Ko ya san Malam Isiyaku? Ya ce eh Baban sa ne.

Ya ce wata rana yaran Malam sun sanya shinge a hanya ba sa barin kowa ya wuce sai wanda suka amince da in da zai je.  Wata rana aka dauko wani yaro za a wuce da shi sai yaran Malam suka tare mai babur din amma ya ki tsayawa sai suka jema musu sanda sai suka fadi yaron ya karye. Daga nan sai mutanen Unguwa suka ce ba su yarda ba sai an cire wannan shingen. Sai rigima ta barke a wannan Unguwar. Kuma Baba shi ne madakin Unguwar sai aka kira shi ya zo wurin. Babana ya je wurin yana ba mutane hakuri sai wani daga cikin almajiran Malam ya ciro wuqa ya caka masa a qafa. Da suka caka masa wuka sai ya fadi. Sai mutane suka korasu. Sai almajiran Malam suka fara harbin mutane da gwafa. Sai mutane suka gudu. Ni da qanina muka je dauko shi. Muka kai shi asibiti aka yi masa magani muka dawo da shi gida.
Ya ce haka suka yi ta jinya har wata hudu kuma an fada musu cewa wuqar tana da guba. Don haka daga baya ya ya mutu. Bayero Dari ya kammala tambayarsa
 
Falana SAN ya tambayeshi ko shi musulmi ne? Ya ce eh. Sunnah ne shi ko Shi'a? Ya ce shi Sunni ne. Ko ya fada wa yan sanda cewa ga wandanda suka kashe babansa? Ya ce bai kai rahoto ba. Zai iya fadin wata da ranar da mahaifinsa ya rasu? Ya ce ba zai iya fada ba. Ko ya san wanda ya ya caka wa Babansa wuka? Ya ce eh Yana ganinsa a cikin tawagar Malam. Ya san sunansa? Ya ce sunansa Ruhana. Ko ya san in da ya ke yanzu? Ya ce yanzu baya ganinsa. Ko Yana da labarin cewa a ranakun 12,13,14 ga watan Disamba sojoji sun kai hari Gyallesu? Ya ce eh ya sani. Ko ka ga yan Shia a wannan rana eh sun shigo har gidansu. Sun shigo ne don boye ko? A'a sun zo qona mana gida ne. Ko sun kona muku gidan? Ba su qona ba. Kana da labarin sojoji sun kone gidan Shaikh Zakzaky kuma suka rushe gidan? Eh ina da labari. Falana SAN ya kammala tambayarsa. Lauyan Malama ya ce bai da tambaya.

Bayero Dari ya ce a nan za su tsaya. Suna neman a basu wata rana saboda suna son kawu GOC ne daga Maiduguri. Falana SAN ya roki kotu da ta ba da ranaku biyu a jere don su kammala kawo shaidunsu a wannan rana.

Kotu ta sanya ranar 25,26 ga watan Janairu don kawi sauran shaidun da suka rage.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu