Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

HALKAR IMAM HASSAN (AS) SUN GUDANAR DA MAULIDIN FIYAYYAN HALITTA A DA'IRAR KADUNA.....

Kaduna press

A jiya 14/11/2020 yan uwa na almajiran Sayyid Zakzaky na halkar Imam hassan (As) sun gudanar da maulidin fiyayyan halitta Annabi Muhammad (s.a.w). An fara taron ne da bu de addu'a da karatun alqur'ani mai girma, sai ziyarar da faretin girmamawa ga Manzon Allah,
Sai a ka gabar da mai jawabi Malam Ahmad Rufa'i, malam ya tabo janibobi da ban da ban ga me da matsayi da darajojin Manzon Allah (S). Malam ya kara da cewa: in na maganar Manzon Allah wa ke maganar sahabbai, Allah manzon Allah ya aiko mana ba sahabbai ba, da ga Manzon Allah sai wasiyan sa, haka nan kuma Allah yayi Alkaurin duk bayan shekara dari Allah zai tayar da Mujaddadi, mun karanta a kitabul bushira,  mun ga irin a bun da a ka yi a zaria.

TA'ALIKI DAGA BAKIN WAKILIN YAN UWA NA DA'IRAR KADUNA
Malam ya bayyana cewa: Hassada rijiyar zam-zam kula da ka'aba duk da ga gidan bamu hashim wannan ne ya sanya hassada a zukatan larawa da yahudawa, ba wai dan ba su san waye manzon Allah ba. Kamar yadda wannan alummar sun san Malam zakzaki da da'awar sa, sa rai.
Sannan ya kara da cewa:
Daga cikin hikimar maulidi, shi ne al'umma su san hakikanin  wane ne Manzon Allah! Su san tarihin sa na hakika, su san suwaye iyalan sa, su waye mabiyan sa, na hakika, a kore duk wani datti da bola da a ka jingina wa Manzon Allah, a matsayin tarihi.
An kuma gabatar da kyauta ga shahidi mai rai, na halkar Imam Hassan (As), sannan a ka yanka alkaki, a ka yi addu'a a ka tashi.
Kd-01/007
Kaduna press
15/11/2020.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu