Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

HALKAR RASULUL AKRAM SUN GUDANAR DA MAULIDIN ANNABI MUHAMMAD (S) A DA'IRAR KADUNA....

A yau lahadi 8/11/2020 wanda yayi daidai da 22 ga watan Rabi'ul Auwal 1442 yan uwa almajiran Sayyid Zakzaky na da'irar Kaduna sun cigaba da gudanar da maulidin fiyayyen halitta (S) na halkar Rasulul Akram.


    Maulud din daya samu halartar daruruwa yan'uwa an gabatar dashine a Unguwan Mu'azu Kaduna. 
     Shareef Ahmad Rufa'i ne ya gabatar da Jawabi a wurin taron.Bayan an bude taron da addu'a sai akayi karatun Al'Qur'ani mai girma sannan sai sha'irai suka baje kolin wakensu sannan aka gabatar da ziyarar Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S) sai babban bako ya fara gabatar da jawabinsa.
Shareef Ahmad Rufa'i ya gabatar da gwala gwalan jawabi akan darajojin Annabi tare da kawo ayoyi da hadisai. Bayan ya kammala sai Pastor Yuhana Buru ya tofa albarkacin bakinsa a taron sannan sai wakilin yan'uwa na Da'irar Kaduna Malam Aliyu Tirmizy yayi ta'aliki. Daga karshe aka yanka alkaki sannan akayi addu'a aka tashi.

  KD-01/010
kaduna Press
©8/11/2020.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu