Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

MATAKAN MANZON ALLAH (S) WAJEN ISAR DA SAKON MUSULUNCI:

Haka dai shekaru yi ta wucewa da'awar Musulunci na ci gaba da yaduwa, duk kuwa da kokarin da Kuraishawa suka yi wajen dakushe sakon, bayan da labarin bayyanar wannan sabon addini, amma dai hakan ya ci tura don sai jama'a ne suke ta ka musulunta. Don haka muna iya kasa kiran da Annabi ya yi a Makka zuwa kashi biyu, wadanda kowannensu yana da na sa rawar da ya taka, su ne kuwa kamar haka:

    Da'awar Sirri.
    Da'awar Sarari.

DA'AWAR SIRRI

Saboda irin adawar da kafiran Makka suke nunawa wa Musulunci, Manzon Allah (s) ya kasance ya kan kira mutane zuwa ga Musulunci ne a boye. A dai dai wannan lokaci sai Allah Ya hore shi da ya kira na kurkusa da shi daga cikin danginsa, don kuwa a lokacin wadanda suka yi imani da shi ba su wuce mutane arba'in ba. Allah Madaukakin Sarki Ya ce masa:

Kuma ka gargadi danginka na kusa. Ka kuma tausasa ga wanda ya bi ka daga muminai. Idan kuwa suka saba maka, sai ka ce: 'hakika ni na barranta daga abin da kuke aikatawa.

(Surar Shu'ara':214-216)

Sai Manzo (s.a.w.a) ya gayyaci danginsa cin abinci. Fara kiransa ke da wuya sai baffansa Abu Lahabi ya yanke shi, ya tsawatar da shi a kan ci gaba da kiran. Sai taro ya watse ba tare da Manzo ya sami daman ci-gaba da kiransa ga mutanensa ba.

A karo na biyu ma dai ya sake tara su, bayan cin abinci ya gabatar musu da wannan sako, a wannan karon ma dai bai samu nasarar isar da abin da ya ke son isarwa, saboda tarwatsa taron da Abu Lahb din ya sake yi. Sai a karo na uku ne Manzon Allah ya sami damar yin magana, inda bayan da aka gama cin abinci, sai ya mike kafin Abu Lahb din ya ce wani abu ya fara da cewa:

Ya ku 'ya'yan Abdul-Mudallibi, lallai Allah Ya aiko ni gare ku da sako na masamman, sai Ya ce: "Kuma ka gargadi danginka na kusa." To ina kiran ku ne zuwa ga kalmomi biyu masu sauki ga harshe (amma) kuma masu nauyi a mizani: Shaidawa babu abin bauta sai Allah, kuma ni ManzonSa ne. wane ne zai amsa min wannan al'amari ya kuma taimake ni a kan aiwatar da shi, sai ya zama dan'uwana, abin wasicina, mataimakina, mai jiran gadona kuma Khalifana a baya na?(1).

Babu dai wani da ya amsa masa daga cikin dangin nasa in ban da Ali bn Abi Talib (a.s), alhali kuwa shi ne ya fi kowa karancin shekaru a gurin, inda ya mike ya ce wa Manzon Allah (s)Ni zan taimake ka a kan wannan al'amari. Sai Manzon Allah (s) ya umarce shi da ya zauna, inda ya sake maimaita wannan bukata tasa, amma dai babu wani wanda ya amsa masan in ban da wannan saurayi Ali (a.s), a wannan karon ma dai Annabin ya ce masa ya zauna. Sai da aka yi haka har sau uku amma babu wani wanda ya ke amsawa sai Ali (a.s) daga nan sai Manzon Allah ya yarda ya kana kuma ya bukaci wadanda suke gurin da su yi masa da'a da biyayya don shi ne zai kasance dan'uwansa, wasiyyinsa, mataimakinsa kana kuma halifansa a bayansa.

DA'AWAR SARARI

To da yake dai an saukar da sakon Musulunci ne ga dukkan duniya ba wai kawai ga wasu mutane na daban ba, don haka babu makawa Manzon Allah ya isar da wannan sako ga kowa da kowa, to amma ta yaya? Sannan kuma dole ne ya jira umarni daga Ubangijinsa. Wannan umarni kuwa ya zo ne a lokacin da Allah Ya saukar da wannan aya: Ka tsage gaskiyar abin da aka umurce ka da shi, kuma ka yi watsi da kafirai. (Surar Hijr:94)

Bayan saukar wannan aya, sai Manzo (s.a.w.a) ya tafi ya hau dutsen Safa da ke Makka, ya tara mutane a wajen, sannan ya bayyana kiransa na Allah ga mutane. Duk da cewa mafi yawan mutane sun gujewa sakon nasa, sai dai wasu sun amsa sun bayar da gaskiya. Haka nan labarin kiran Allah ya shiga kowane gida. Daga mutanen da suka ba da gaskiyar har da dangin Annabi (s) irinsu Ja'afar bn Abi Talib, Ubaidah bn Harith da dai sauransu.

Amma irin wannan ci gaba da Musuluncin ke samu ya sanya mushirikan Makka cikin matukar bakin ciki, saboda tsoron kubucewar mulkinsu, don haka sai suka dauki matakan gallazawa duk wanda ya karbi wannan addini, ba don komai ba sai don rashin wata hujja da za su kare bautar gunki ko kuma hana mutane karbar Musulunci. Daga cikin irin mutanen da aka gallazawa akwai Bilal al-Habashi, Suhaib, Ammar bn Yasir da mahaifansa Yasir da Sumayya da dai sauransu.

Kafin dai a kai ga gallazawan, kafiran Makkan sun yi kokarin raba al'umma din da Manzon Allah (s) ta hanya nuna musu cewa shi makaryaci, mawaki, mai sihiri da mahaukaci; suka shiga yi masa izgili. Sai dai wannan bai raunana Manzon Allah (s.a.w.a) ya hana shi ci-gaba da kira zuwa ga gaskiya ba; don haka sai suka dauki matakin jawo hankalin shi ta hanyar bijiro masa abubuwan jan-hankali da hure kunne, na daga mulki, shugabanci da dukiya.

Sai dai Manzo (s.a.w.a) ya ki amsar duk wananna yana mai ci gaba da abin da ya sa a gaba; don haka sai suka dauki matakin kuntata masa da iyalinsa da dukkan wadanda suka yi imani da shi, sai dai kuma a nan ma dai kokarinsu ya tafi a banza a sakamakon gwarzantakar Manzo da tsayuwarsa bisa gaskiya tare da kariyar Abu Talib, matarsa Khadija da kuma Aliyu bn Abi Talib gare shi. Har ma an ruwaito shi yana cewa wannan addini na Musulunci ya tsaya da kafarsa ne saboda kariya irinta Abu Talib, dukiyar Khadijah da kuma takobin Ali (a.s).

____________
(1)- Ibin Athir, cikin al-Kamil, juzu'i na 2, shafi na 24; da Biharul-Anwar, juzu'i na 18, shafi na 164; da Fiqihul-Sirah, na Sheikh Muhammad Gazzali, shafi na 102.


Kd-001/007
Kaduna Press.
20/10/2020

Post a Comment

0 Comments

Close Menu