Yan uwa harisawa almajiran sheikh Zakzaki na imam bakir zone kaduna unit sun gudanar da taron karawa juna sa ni, na wuni biyu (2) a da'irar kaduna.


an fara taron ne da bude wa da addu'a, da karatun alqur'ani, 


An kuma gabatar da jawabi mai taken: Makasudin taro da hadafin samar da rundunar Amirul Muminin, da ga nan kuma a ka karanta ka'idojin harisanci.

Har wala yau kuma an motsa jiki. San nan a ka gabatar da jawabi mai taken: Mujahada, da kuma kutsan makiya harka islamiyya ga yayan harka.