KADUNA PRESS

Yau laraba 11/11/2020 Yan uwa almajiran Sayyid Zakzaky (H) na halkan Imam Mahdi (Q.s) dake da'irar Kaduna sun gudanar da maulud na fiyayyen hallitta Annabi Muhammad (s.a.w.w). Bayan bude taro da addu'a wanda Malam Aliyu bakin ruwa yayi sai majalisin mawaka daga bakin malam Auwal Alhassan (k/mashi). Angabatar da mai jawabi wakilin yan uwa na grain jaduna malam Aliyu Umar (Tirmizi).
Wanda shugaban halkan mal Auwal rigasa ya gabatar.
Malam Aliyu tirmizi ya yi bayani a kan lokacin da aka haifi Annabi, sanan yace: shi Annabi Muhammad (s.a.w.w) shi tun farkon hallittar sa, Manzo a ka haifa, sabo da haka shi Annabi yazama Manzon tun adamu yana tsakanin ruhi.
In dai kana san kasan waye Annabi to dole sai kabiyo tarihi na hakika bawai irrin tarihin da a ke ma yara ba a makaranta ba, cewa an haifeshi a Makkah kuma mahaifin sa yarasu kuma maraya ne.
Indai haka ne to baza ka gane waye Annabi Muhammad ba sai ma kaji kaman mutun ne kaman kowa.
A wajan wasuma sai suji wani yafishi sabo da ba a kawo hakikkanin waye Manzon Allah ba. Sabo da Manzon Allah An halice shi sama da shekara dubu hudu kafin a hallici Annabi adamu, sabo da haka ya kamata musan tarihi na musan man a kan Manzon Allah.
Asallin tarin Manzon Allah duk a cikin mu muka fara batawa. Wai Annabi bai ce ku kawo a bun rubutu ba? zan rubuta a bun da in kuka rike ba zaku bata ba!
Mai yasa suka ki? Shi yasa yahudawa su ke ta jujjuya tarihi suke a bun da suka ga dama a kan Manzon Allah.
Wanan wani Christian ya ke fadan haka
An gabatar da walima da kyaututtuka sannan a ka yanka Alkali, a ka rufe taron da addu'ah a ka tashi.
Kaduna press
11/11/2020.

https://www.instagram.com/p/CHdf3IasXkH/?igshid=1ltjjrqepl1xc