Kaduna Press
©13/12/2020

A dai_dai irin wannan ranar ne ta 13 ga watan december 2015  sojoji suka shahadantar da Shaheed Malam Ibrahim badiko, a yunkurin su na kisan kiyashi a akan almajiran shaikh zakzaky (h). 

Shaheed Malam Ibrahim badikko yayi shahada ne a lokacin da sojojin kasarna suka kai hari  gidan jagoran harkar Musulunci Sayyid Ibrahim Zakzaky, (H) da ke anguwar gyallesu.

 Sun kashe almajiran Sayyid Zakzaky sama da dubub(1000+) kuma yayan sa uku, da kona yayarsa da ranta, sukayi masu kabarin bai daya, wato (massgrab.

Rayuwar Shaheed Malam Ibrahim badikko, ya kasance, kusan a karatu ya kare rayuwar sa, yana koyarwa da asuba 6:30am, zuwa 7:15am, a masallaci, sannan ya tafi makarata ne man ilimi da misalin karfe takwas 8:00am, na safe, ya dawo kafe 12:00pm, ya koyar da matan sure karfe 12:30pm, da yamma kuma 4:30pm ya koyar da masu hadda, da misalin karfe 8:00pm ya koyar da iyaye maza, sannan kowace ranar asabar karatun matasan halkar imam Hussain kaduna, karfe 10:00am zuwa 1:30pm, ga kuma iyali har uku, ya yara kusan 8.

Shaheed Malam Ibrahim Badiko mutum ne mai yawan kyauta, sannan baya daga murya a maganar sa, yana magana cikin tausasawa da girmamawa, ga kuma karamci sosan gaskiya, hatta da makiyan sa sun masa shaida, kuma sunyi kukan shahadar sa.

A kwai wasu wadan da girma ya kamasu (tsufa), basa iya fita neman kudi, shahid ya yi asusu ya natara kudi, yana musu albashi, dubu biyar biyar (#5000)duk wata, sai bayan shahadar sa ne wasu suka sa ni.
magaran gaskiya a halin sa ba na kushewa.

Mun rokon Allah ya amshi shahadar sa, ya tsinewa, wadanda suka zubar da jinin sa, da kawo karshen wannan azzalumar hukumar don alfarmar Manzo (S) da Iyalan gidan sa tsarkaka.

Kaduna Press
©13/12/2020