Da yanamacin yau juma'a 18 ga watan 12 shekar 2020 yan uwa Musulimi almajiran Shaikh Zakzaky na garin kaduna sun fito Muzaharar lumana, don cigaba da kura ga gwamnatin Najeriya da ta saki jagoran harkar Musulunci Sheikh Zakzaky da mai dakin sa, wanda da take tsare su, ba tare da laifin komai ba.
Sheikh Zakzaky da mai dakin sa na tsare ne tun bayan kisan kiyashi da sojojin Najeriya sukayi a ranar 12 ga watan 12 shekar 2015, a garin Zaria. 

Muzaharar ta daga ne a dai dai gwamna road da ke kan titin  Nmadi Azikway baypass a nan cikin garin Kaduna.  An yi Muzaharar cikin tsari da nizami ana rera waken free zakzaky kamar yanda aka saba. An yi lafiya an tashi lafiya.

Kaduna press
18/12/2020.