A jiya  Asabar 19/12/2020, Yan uwa matasa almajiran Sayyid Zakzaky (H)
Na da'irar Kaduna sun gudanar da mauludin Sayyida Zainab (A.s)
Yar Zayyid Zahra (As).
Mauludin yasamu hallartan wakilan matasa na ciki da wajan garin kaduna.
 Mai jawabi malama Fatima Mujahidah.
Ta albarkaci wajan da gwala gwalan jawabi akan rayuwan Sayyida Zainab (As),
In da take cewa: ita Sayyida Zainab jarumace kuma abun koyi takowani janibi na rayuwa.
Sabo da Sayyida tasha tarbiya waje biyu na farko tayi rayuwa da kakanta Annabi Muhammad (s.a.w .w), Shekara biyar kafin wafatinsa.
Sanan kuma tayi shekara talatin da biyar da babanta Imam Ali (As), Shiyasa duk wani ilimi da Sayyida Zahara tasamu to tashayar da Sayyida Zainab (As),
Shiyasa tasamu juriya a duk lokaci da wani musiba ta tunkarota.

Sayyida Zainab tayi aure Kuma ta auri Abdullahi, Sanan ta haifi yara biyar cikin su Akwai Abbas. Sanan lokacin da Imam Ali zai aurar da ita sai da yayi sharadi guda biyar, Daya daga ciki shine bada kariya ga dan uwanta Imam Hussein a filin Karbala,
Shiyasa lokacin da take karama duk inda zakaga Imam Hussein to zakaga Sayyida Zainab, hakan yasa wata rana sai Manzon Allah (S) ya kalli Sayyida Zainab kawai sai yafara hawaye, koda aka tambayeshi sai yake cewa duk wani masifa da zata sauka a fillin Karbala to agabanta zai kasance.
Ita Sayyida Zainab Allah yabawa Imam Hussein a matsayin mataimakiya.
Wata rana manzon Allah yazo gida sai yaji Sayyida Zainab (As) tana karatun Alqur'ani
Sai ta zo dai dai suratul Maryam sai Annabi ya tsaya yayi mata tafser na suran aya ta farko shine yake magana akan musiba na Karbala, Kaga kenan Sayyida Zainab bawai mace kawai bace a'a, a bun koyi ne ga ma'abota addini tun daga dakewarta dama juriyan imani datakedashi.

Malama taja hankali a kan rashin baiwa matasa goyan baya wajan gudanar da aikin su na yau da kullin na addini.
Sanan tayi addu'a ga mahalartan taron,
da kuma irrin jajircewa da akeyi wajan gudanar da wanan munasabobi a wanan da'irar na Kaduna duk da yanayin da a ke ciki na jarawa da sauran su.

MALAM ALIYU BAKIN RUWA SHI NE YA GABATAR DA TA'ALIKI A WAJEN
Malamin ya fara ne da jan hankalin Matasa a kanyin abu dan Allah. Duk abun da zamuyi ya zama dan Allah mu keyi bawai mujicewa munayi ne dan jarumtaba.

Sanan ya ja hankalin Matasa cewa: sunyi kokari sosai wajan gudanar da wanan maulud, musanman wajan sanya gasan wake da matasan sukayi akan rayuwan sayyida zainab (As).

Inda daga karshe aka raba kyau daga na daya zuwa na uku, sanan aka yanka alkaki 
Akayi addu'a 
Anyi lfy antashi lfy

Kaduna press
19/12/2020
Kd-001/006.