KADUNA PRESS.

Kamar yadda a ka saba lokaci bayan lokaci yan uwa Almajiran sheikh Zakzaki na fitowa muzahar lumana, dan kira ga gwamnatin Najeriya da ta saki jagoran harkar musulunci da mai dakin sa, wannda take rike da su, ba tare da laifin komai ba,  said dai yau talata 08/12/2020, jami'an tsaro Najeriya 'yan ina da-kisan da hadin gwiwar yan kato da gora, sun afkawa 'yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzakiy (H) da harbin kan mai uwa da wabi, da harsasai masu rai.
Jami'an tsaron dai sun afka ne bayan an baro kabala junction a dede dutsenma kafin su karasa kagoro by express.
Tun farko dai yan kato da gora sun fara jifan masu muzaharar ne kafin daga bisani yan sanda suka fara harba tiyagas da harsasai masu rai.
I zuwa hada wannan rahoton dai bamu samu labarin an raunata ko kuma kama kowa ba.

-KNPRCD 06.
-08/12/2020.