GAGARUMAR MUZAHARAR FREE ZAKZAKIY A KADUNA-KADUNA PRESS.

Da yanmacin yau laraba 16 ga watan 12 Shekarar 2020 da misalin karfe 04:00pm na yamma, daruruwan yan'uwa Almajiran Sheikh Zakzaky, na garin Kaduna sun fitowa domin cigaba da yin kira ga gwamnatin  Buhari da ta gaggauta sakin jagoran harkar musulunci a najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa, wanda take cigaba da tsarewa tsawon shekaru biyar (5) ba tare da laifin komai ba.Tun bayan harin ta'addancin sojojin Najeriya karkashin gwamnatin janar Buhari ta yi a ranar 12-14/12/2015, da kaisan mabiyan sa sama da dubu, ciki har da ‘ya‘yansa uku, da kona yayar sa da ranta a gaban sa, suka tsare daliban sa daruruwa.A shekarar 2016 babban kotun dake Abuja ta wanke shi, tace: baiyi laifin komai ba, asake shi amma gwamnatin taki, tayi kunnen uwar shegu da maganar.

 

Yanzu haka Sheikh Zakzaky (H) da iyalin sa, na gidan kurkun Kaduna, ba tare da wani dalili ba.


Muzaharar dai ta daga ne a dai dai Kano road da ke nan tsakiyar garin kaduna, anyi lafiya an tashi lafiya.

-KNPRCD 16.

-16/12/2020.