A jiya Asabar 12/12/2020 a ke cika shekaru biyar da ta'addancin sojojin Najeriya, a garin zaria, Yan'uwa musulmi Almajiran Shaikh Ibrahim zakzaky (H) na garin kaduna sun fito domin tinawa da kuma kira ga al'umar duniya da su fahimci girman ta'addancin da sojojin najeria suka aikata, a kan sheikh Zakzaky da almajiransa  a ranar 12 ga watan 12 shekar 2015. kuma da nuna rashin amincewar su da cigaba da tsare shaikh da a ke yi, ba bisa ka'ida ba. 
An Gudanar da Muzaharan ne da misalin karfe 3:00pm a kofar kaduna polytechnic da ke Tudun wada. Muzahar ya samu halartan daruruwan jama'a maza da mata, masu son ayi adalci daga kowani janibi, a fadin jahar. 
An tafi cikin tsari, tare da Kira ga. Gwamnatin wanna kasar data gaggauta sakin Jagoran Harkan Musulinci Sayyed zakzaky wanda take Tsare dashi a gidan kurkukun Kaduna tare da matarsa Malama zeenatudin Ibrahim ba tare da lafin komai ba, an yi Muzaharan Lafiya an tashi Lafiya ga wasu daga cikin hotunan muzaharan da muka dauko muku a wajan
Kaduna press
12/12/2020