A yau 25/12/2020 al'ummar kirista ke bikin zagayowar haihuwar Annabi Isa ( a.s.) a fading duniya.
Annabi ne wanda ya kiraye jinsin 'yan-adam zuwa ga shimfida adalci da daidaito a tsakaninsu da kuma bautar ubangiji. Wannan rana ce ta haihuwar ma'abocin girma da albarka. Rana ce wacce Ubangiji ya busa ruhin Annabi Isa (a.s.) a cikin maryam (.sa.) domin ya zama mai yin bushara da adalci. 

Kaduna Press: Muna isar da sakon yaya murnar zuwan wannan rana gare ku, al'ammar kirista, musamman ma Pastor Yohana Buru, a wannan lokacin mabiya addinin Kiristanci suna fadi tashin yin bikin zagayowar haihuwar Annabi Isa (.a.s.) ta kirsimati. Suna kawata Coci da biranensu da fitilu da kuma bishiyar kirsimati wacce aka yi wa kawa. Sai dai ba zamu manta da wahalhalun da wasu yankuna na duniya su ke ciki ba, sanadin haka ya rage musu jin dadin wannan biki. Mu sheda ne akan cewa wannan zamanin da mu ke rayuwa a cikinsa ya fi wanda ya gabace shi yawan tashe- tshen hankula, Muna ganin yadda kananan yaran palasdinu su ke rayuwa a karkashin killacewar da Yahudawan Sahayoniya, su ka yi musu a yankin Gaza. . Suna fama da sanyi mai tsanani da dusar kankara da ke zuba ba tare da sun sami makamashin dumama dakunansu da gidajensu ba, Suna fama da yinwa ba tare da sun sami abincin ba. A cikin irin wannan yanyin manyan kasashe masu takama da karfin soja wadanda kuma su ke riya cewa su mabiyan Annabi Isa (a.s.) ne suna ci gaba da zaluntar kasashe masu rauni na duniya, A aikace babu wani abu da ya ke nuni da cewa suna bin koyarwar Annabi Isa (a.s.) A wannan lokacin kasashen duniya sun gaji da matsalar rashin tsaro wacce ta samo tushe daga yake-yake. A wannan lokacin ruhin mutum yana sauraron samun nutsuwa da kwanciyar hankali da zaman lafiya. Ranar haihuwar annabi isa (a.s.) dama ce mai muhimmanci ta yin tunani a kan samun shiriya daga koyarwar annabawan Ubangiji ta zaman tare cikin kwanciyar hankali. . Garin Nasiriyya karami ne da ya ke a cikin palasdinu, a cikin wannan karamin garin ne wata buduruwa mai suna maryam wacce ta ke ma'abociyar tsarki da tsoron Allah ta rayu, nufin Ubangiji da kudurarsa ya so wannan mace ma'abociyar karama da ta za maza mahaifiyar Al-masihu daya daga cikin manyan Annabawan Allah. Maryam ta kasance mace tsarkakkiya, ma'asumiya, kamila wacce ba ta da nakasa a tare da ita, ta kasance mai kaunar Ubangiji da kuma tsarkake bauta a gare shi, tana cikin irin wannan halin na bautar Ubangiji ne ita kadai mala'ika Jibrilu ya sauka a gareta dauke da sako daga mahaliccin sammai da kassai akan ya yi mata busharar haihuwar mai ceto. . Alkur'ani maigirma da littafatin Linjila sun bada wannan labari.

Ya zo a cikin suratu Maryam a kur'ani mai girma cewa: Kuma ka ambaci labarin Maryamu a wannan littafi lokacin da ta kauracewa mutanenta ta koma wani wuri a nahiyar gabas, sai ta sa shamaki tsakaninta da su to sai muka aiko mata da Ruhinmu ya bayyanar mata a cikin surar mutum sak, a cikin wata ayar ta wannan surar Allah ta'ala ya bada labarin muhawarar da ta gudanta tsakanin Maryam da kuma mala'ika Jibra'ilu. Wannan dan sako na Ubangiji ya fada mata cewa: "Ni manzo ne na Ubangiji kawai na zo in kawo maki baiwar da ( namiji) tsarkakakke, haihuwar Annabi Isa (a.s.) ba tare da mahaifi ba aya ce daga cikin manyan ayoyin Ubangiji da kuma karfin ikonsa ta yadda ya halicci wasu bayinsa ta hanyar al'ada da abinda aka saba da shi. Wasu daga cikin mutane da su ka kidima da mamakin yadda aka haifi Annabi Isa (a.s) ya sa sun ba shi matsayin Ubangiji, wasu daga cikin yahudawa kuwa sun tuhumi maryam ne da aikata abinda bai dace ba. Ubangiji madaukaki a cikin suratu Ali-Imrana aya ta 59 yana fadin cewa: hakika misalin Isa a wurin Allah kamar misalin Adamu ne; ya halicce shi ne daga turbaya, sannan ya ce da shi ka kasance sai kawai ya kasance. 
Wadannan abubuwan gaskiya ne daga Ubangijinka, saboda haka kada ka kasance daga masu kokwanto," Annabi Isa (a.s.) yana daga cikin zuriyar Annabi Dauda, mahaifiyarsa maryam (a.s) daya ce daga cikin mata hudu zababbu a gidan aljanna. Nufin Ubangiji ya sa Annabi Isa(a.s.) ya zama mai yin bushara da adalci da aikin kwarai a cikin duniya. Wannan annabi na Allah wanda aka haifa ta hanyar da ta sabawa al'ada ya kasance wanda mu'ujiza ta ke gudana a hannunsa, a lokacin da ya ke cikin tsumman goyo ya yi magana domin kare mahaifiyarsa daga tuhumar da yahudawa su ka yi mata. Aya ta 30 zuwa ta 33 a cikin suratul- Maryam tana fadin cewa: sai ya ce hakika ni bawan Allah ne, Ya bani Littafi ya kuma mayar da ni Annabi, ya kuma sanya ni mai albarka a duk inda na ke, kuma ya umarce ni da yin salla da kuma bada zakka, matukar ina da rai. Kuma mai biyayya ga mahaifiyarsa bai kuma sa ni mai girman kai mai sabo ba, Amincin Allah kuma ya tabbata a gare ni ranar da aka haife ni da ranar da zan mutu da kuma ranar da za'a tashe ni rayayye. 

Muhimmin abinda kur'ani yake jaddadawa akansa shi ne cewa Annabi Isa (a.s.) da ya ke ma'abocin ilimi da dimbin sa ni da mu'ujiza bawa ne mai kaskantar da kai ga mahaliccinsa. Rayar da matattu da kuma warkar da makafi suna daga cikin mu'ujizojin Annabi Isa (.a.s.) Aya ta 49 a cikin Suratu Ali Imran ta yi ishara da yadda Annabi Isa (a.s.) ya ke gina tsuntsaye daga yunbu sannan ya hura musu ruhi da izinin Allah. 

An haifi annabi a cikin tsarki kuma yayi rayuwa cikin tsarki ba tare da sabon Ubangiji ba, ya kasance mai kyautatawa mutane da jin kan marasa galihu da fada da zalunci. Matsayin Annabi Isa (a.s.) a wurin Allah ya kai ga idan ya daga hannu sama ya yi addu'a za'a saukar da abinci saboda shi da sahabbansa. Isa (a.s.) ya kawar da jahilci daga tsakanin mutane da kuma sanar da su abubuwa masu kyawu a rayuwa. Ya kasance mai watsi da abin duniya da kuma kin jinin zalunci da kaunar shimfida adalci, a cikin riwayoyin Musulunci ya zo cewa Annabi Isa (a.s.) ya fadawa sahabbansa cewa: Ya ku hawariyawa ku nemi kusantar Ubangiji ta hanyar nuna kiyayya da masu sabo, ku karace shi ta hanyar nisantar su. Isa (a.s.) ya kasance ma'abocin kyawawan halaye na koli, Yana shiga cikin mutane da zama da makiyaya da manoma da kuma yin wa'azi a cikin maja'mi'a da kasuwanni da kuma kiran yahudawa da su nesanci aikata munanan ayyuka, sannu a hankali mutane su ka fahimci cewa ya bambanta da sauran masu wa'azi da aka saba gani a cikin Banu-Isra'ila, saboda haka Annabi ne kuma zababben Ubangji na kwarai. . Wanda ya ke yin kira zuwa ga adalci da yafiya da jin kai da tausayi a tsakanin mutane, Yana fadin cewa: duk wanda yake yin girman kai to zai wulakanta, wanda duk ya ke kaskantar da kansa zai daukaka. Ya zo a cikin tarihin Annabi Isa (a.s.) cewa: Wata rana Annabi Isa (a.s.) yana tafiya tare da sahabbansa zuwa wani gari, a kan hanyarsu suka ci karo da taska ta dukiya, Wasu daga cikin huriyawa su ka nuna kwadayin wannan taskar saboda haka su ka dakatar da tafiyar da su ke yi da Annabi Isa (a.s.) domin su dauki wannan taskar. Annabi Isa (a.s.) ya fada musu cewa: Wannan taskar babu abinda ya ke tattare da ita idan ba wahala ba. Amma na san inda taska ta ke a cikin wannan garin wacce ba ta tare da wahala kuma za mu nufi inda ya ke. Annabi Isa ( a.s.) ya shiga cikin wannan garin inda ya hadu da talakawa da marasa galihu sannan ya kyautata musu. Ya kuma warkar da wani karamin yaro da a ka haife shi da makanta bisa izinin Ubangiji wanda kuma a cikin kankanen lokaci ya zama shugaban wannan garin Wannan matashin ya tsaya a gaban Annabi Isa (a.s) ya fada masa cewa: Kai da ka ke iya warkar da mai cuta sannan kuma ya kai ga zama ma'abocin iko me ya sa kai ka ke gamsuwa da kadan?"  Annabi Isa (.a.s.) ya ba shi jawabi da cewa: Abin duniya da ya ke mai karewa yana da kima ne a idanun wadanda ba su da labarin jin dadin lahira da ya ke dawwamamme har abada. Wanda ka gada a mukamin da ka ke da shi yanzu haka yana kwance a cikin kasa kuma babu wanda ya ke ko ambatonsa, Ina amfanin mulkin da za'a mance da shi?" Wannan saurayi ya nutse cikin tunani, bayan wani lokaci ya fadi cewa:" Me ya sa ka yi mani jagora wajen kaiwa ga matsayin da zai kare ka hana ni kaiwa ga dawwamammen jin dadi?" Annabi Isa (a.s.) ya ba shi jawabi da cewa:" Ina so ne ka koyi darasi ta yadda za ka zama mai zabin bin hanyar gaskiya da kanka. Matashi ya yi watsi da sarauta ya bi Annabi Isa (a.s.) shi kuwa Annabi Isa (a.s.) ya kai shi wurin sahabbansa huriyawa ya fada musu cewa: Wannan matashin maraya shi ne taskar da na ke nema wanda a cikin takaitaccen lokaci ya kai ga samun sarauta, amma ya yi watsi da dukkan wannan jin dadin na zahiri ya biyo ni. Ku kuwa bayan tsawon shekaru kuna biyayya gare ni kun yi watsi da ni ku ka nufi taska." A duk inda Annabi Isa ya je yana shiryar da mutane akan hanyar ayyukan kwarai da kuma gaskiya. Muna masu kyakkyawan fatan cewa dukkan wadanda su ke kiran kansu masu biyayya ga Al-masihu za su yi aiki da abubuwan da dukkan Annabawan da Allah ya aiko su ka yi tarayya a kansu wanda shine bautar Ubangiji makadaici da neman shimfida adalci. Su zama masu yin gaskiya da kuma aiki domin tabbatar da zaman lafiya a cikin duniya baki daya. 

Amincin Allah ya tabbata ga Annabi Isa (a.s.) da mahaifiyarsa Maryam (a.s.). 

Muna taya kowa da kowa murnar wannan rana ta haihuwar Annabi Isa Al-Masihu (a.s.).

Kaduna Press
25/12/2020